Zargin Satar N27bn: Kotu Saki Tsohon Gwamna, Ta Gindaya Sharuda Belinsa
- Wata babbar kotun tarayya ta ba da belin tsohon gwamnan jihar Taraba da ake zargi da karkatar da makudan kudi N27bn
- Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku kan zargin karkatar da kudin a lokacin da yake mulki
- Legit ta tattauna da wani lauya, Marwan Abdulhakam domin yin karin haske kan yadda ake ba da belin wadanda ake zargi da satar kudi mai yawa a kan kudi kadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rahotanni na nuni da da cewa wata kotu a birnin tarayya Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan jihar Taraba.
Tsohon gwamna Darius Ishaku ya shaki yanci ne bayan EFCC ta cafke shi kan zargin karkatar da kudi har N27bn a ofis.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan ne bisa zarge zarge 15 da suka shafi karkatar da kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ba da belin tsohon gwamnan Taraba
Wata kotun tarayya da take zaune a birnin tarayya Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku a yau Alhamis.
Rahotan gidan talabijin Channels Television na nuni da cewa an ba da belin Ishaku ne a kan kudi N150m bisa zargin da ake yi masa.
Sharadin ba da belin Darius Ishaku
A ranar Litinin, Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs yaki amincewa da ba da belin Darius Ishaku kan cewa dole sai ya yi rubutu da kansa.
Amma a zaman kotun na yau Alhamis, kotun ta ba da belin tsohon gwamnan bisa sharadin kawo mutum biyu da suke zaune a birnin tarayya Abuja.
Yaushe za a cigaba da shari'ar EFCC da Ishaku?
Bayan ba da belin, kotun ta bayyana cewa za a cigaba da sauraron shari'ar a ranar 4 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Haka zalika kotun ta ba da belin wani jami'in gwamnatin Taraba, Bello Yero da ake zargi tare suka hada baki da Darius Ishaku.
Legit ta tattauna da lauya
Wani lauya, Marwan Abdulhakam ya zantawa Legit cewa dalilin da yasa ake ba da beli shi ne wanda ake zargi yana matsayin wanda ba a kama da laifi dumu-dumu ba.
Marwan ya kara da cewa ba da belin mutum ba yana nufin an sake shi ba ne kuma kudin beli ba a madadin kudin da ake zarginsa ake karba ba.
EFCC za ta binciki tsohon gwamna
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa za ta yi bincike kan zargin da ake yi wa Bello Matawalle.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa za ta binciki zargin da ake yi wa tsohon gwamnan na Zamfara kan karkatar da kuɗin jiharsa da yake mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng