Ministan Tinubu Ya Koka da Karuwar Talauci a Arewa duk da Yan Siyasarta na Gwamnati

Ministan Tinubu Ya Koka da Karuwar Talauci a Arewa duk da Yan Siyasarta na Gwamnati

  • Karamin Ministan noma, Aliyu Sabi Abdullahi ya yi takaicin yadda karuwar arzikin kasa bai nuna a Arewa ba
  • Tsohon Sanatan ya bayyana haka ne a wata laccar gabanin taron tsofaffin daliban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria
  • Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce Arewa ta yi zarra wajen filin noma kuma ta fi kowane yanki a Afrika yawan dabbobi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar talauci a Arewacin kasar nan.

Karamin Ministan noma, Aliyu Sabi Abdullahi da ya bayyana haka, ya kara da cewa an samu karuwar tattalin arziki na GDP.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Sanata
Minista ya yi takaicin karuwar talauci a Arewa Hoto: Sen Aliyu Sabi Abdullahi
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Ministan da ya samu wakilcin babban sakataren cibiyar Agricultural Research Council of Nigeria, Farfesa Garba Hamidu Sharubutu ya fadi haka ne a laccar gabanin taron tsofaffin daliban jami'ar ABU.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai talauci a Arewa:" Minista

Karamin Ministan noma, Aliyu Sabi Abdullahi ya ce arzikin kasa na GDP ya karu da 19%, amma hakan bai nuna a rayuwar mazauna Arewa ba.

Sanata Sabi ya ce Arewa tafi duk nahiyar Afrika yawan dabbobi, inda ake da shanu miliyan 19.5, awaki miliyan 72.5, tumaki miliyan 41.3 da raƙumi 28,000.

Ministan ya koka kan yadda hakan bai kawo yalwar arziki tsakanin mazauna yankin ba.

Arewa: Minista ya yi takaicin karuwar talauci

Karamin Minista, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce akwai tarin arzikin kasa da ya sa Arewa ta yi fice a bangaren noma, amma hakan bai hana karuwar talauci ba.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

Sabi Abdullahi ya ce an san Arewa da noman muhimman kayan abinci, saboda haka akwai bukatar a hada hannu wajen nemo hanyoyin warware matsalar.

"Akwai talauci a ko ina:" Tinubu

A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince akwai talauci a Najeriya, amma ba 'yan kasar nan ne kawai talaucin ya addaba ba.

Shugaba Tinubu ya bayyana wasu hanyoyi da za a bi wajen magance matsalar, inda ya ce sai an kawar da ayyukan ta'addanci domin manoma su samar da abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.