Fada Ya Kaure, Manyan Ƴan Bindigan Arewa da Yaransu Akalla 20 Sun Baƙunci Lahira

Fada Ya Kaure, Manyan Ƴan Bindigan Arewa da Yaransu Akalla 20 Sun Baƙunci Lahira

  • Kungiyoyin ƴan ta'adda sun yi kazamin artabu tsakanunsu a yankin Ɗan Ali da ke karamar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina
  • Bayanan sirri sun nuna cewa ƴan bindiga akalla 20 ne suka baƙunci lahira a faɗan wanda ya auku da safiyar ranar Larabar nan
  • Rahotanni sun tabbatar da daga cikin waɗanda aka kashe har da wasu daga cikin jagororin ƴan bindigan da suke fitini jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Wasu ƙungiyoyin 'yan bindiga masu adawa da juna sun yi artabu a jihar Katsina, akalla ƴan ta'adda 20 sun baƙunci lahira.

Rahotanni sun nuna ƴan bindigar sun kaure da faɗa tare da karkashe junansu da safiyar ranar Laraba a kauyen Ɗan Ali da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno ana murnar samun 'yancin kai

Taswirar Katsina.
An rage mugun iri yayin da wasu kungiyoyin ƴan bindiga suka yi arangama a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kuna mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe ƴan bindiga 20 a jihar Katsina

Ya ce ya samu labarin daga cikin waɗanda suka mutu a arangamar har da wasu daga cikin jagororin ƴan ta'addan.

Ya ƙara da cewa faɗan ya faru ne tsakanin ƙungiyar ƴan bindiga karkashin Mai Nore da mayakan kungiyar Buzaro.

"Da sanyin safiyar yau (jiya Laraba), wani kazamin fada ya barke tsakanin kungiyar ƴan bindiga ta Mai Nore da kungiyar Buzaro a yankin Dan-Ali.
"A cewar wasu majiyoyin leken asiri, faɗan ya zama silar rage mugun iri, inda aka samu gawarwakin ƴan bindiga sama da 20 a wurin."

- Zagazola Makama.

Yadda ƴan bindigar suka yaƙi juna

Ganau da suka ga abin da ya faru sun ce faɗan da ƴan ta'addan suka yi a tsakaninsu ya yi tsanani sosai domin an riƙa jin ƙarar harbe-hare a ilahirin yankin.

Kara karanta wannan

Ranar ƴanci: Shugaba Tinubu ya yi magana kan farashin kayan abinci, ya faɗi mafita

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojojin Najeriya ta ƙara matsa ƙaimi wajen kakkaɓe ƴan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Yan bindiga sun shiga asibiti a Katsina

A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun kai hari babban asibitin da ke ƙaramar hukumar Kurfi a jihar Katsina ranar Laraba da ta gabata da daddare.

Bayanai sun nuna maharan sun harbi mai gadi, sun sace mata hudu a ciki har da matar wani likita da ke aikin dare a asibitin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262