An Samu Karin Bayani kan Yadda ICPC Ta Kwato N13bn da Aka Handame a Wata 1
- Yayin da yan Najeriya ke kokawa game da yawan cin hanci da rashawa, hukumar ICPC ta samu galaba kan wasu barayi a Najeriya
- Hukumar yaki da rashawar ta tabbatar da kwato makudan kudi har N13bn da aka yi baba-kere a kansu a watan Satumar 2024 da ta gabata
- Shugaban hukumar, Adamu Aliyu shi ya tabbatar da haka inda ya fadi wasu hanyoyin inganta bincikensu na zamani da sauran bangarori
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta yi magana kan makudan kudi da aka handame a Najeriya.
Hukumar ta ce ta yi nasarar kwato har N13bn da wasu tsiraru suka yi sama da fadi da su a watan Satumban 2024 dinnan da ta gabata.
ICPC ta kwato N13bn da aka karkatar
Shugaban hukumar, Adamu Aliyu shi ya tabbatar da haka a jiya Talata 1 ga watan Oktoban 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai hukumar ba ta fayyace ma'aikatu ko kuma mutanen da ake zargi da handame kudin ba, Vanguard ta ruwaito.
Hukumar ta tabbatar da himmatuwarta wurin yaki da cin hanci domin samar da tsaftatacciyar al'umma.
Hukumar ICPC za ta inganta hanyoyin bincikenta
"A shekarar bara, ICPC ta yi kokari matuka wurin yaki da cin hanci, misali, mun yi nasarar kwato N13bn da aka karkatar a watan Satumbar 2024."
"Wannan na daga kadan daga cikin ayyuakan da muke yi domin tabbatar da abin da muka sanya a gaba ba tare da gajiyawa ba."
- Adamu Aliyu
Adamu ya kuma bayyana shirin hukumar na inganta ayyukanta wurin zamanantar da hanyoyin bincikenta da sauran hanyoyin dakile cin hanci a Najeriya.
ICPC ta gurfanar da jami'in NSCDC
Kun ji cewa Hukumar mai yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta jawo an daure wani kwamandan NSCDC bisa laifin zamba cikin aminci.
Kwamandan mai suna Christopher Oluchukwu ya karbi makudan kudi a wurin mutane da dama da sunan sama musu aiki.
Lauyan hukumar ICPC, Ibrahim Garba ya bayyana yadda ayyukan zamba da Christopher ya yi suka sabawa dokar kasa.
Asali: Legit.ng