Sanata Ndume Ya Faɗawa Tinubu Yadda Za a Yaki da Ta'addanci cikin Sauƙi

Sanata Ndume Ya Faɗawa Tinubu Yadda Za a Yaki da Ta'addanci cikin Sauƙi

  • Sanata Ali Ndume ya shawarci gwamnatin tarayya ta dauko hayar sojojin da za su kakkabe yan ta'adda a Najeriya
  • Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawan kasar nan ya ce sojojin haya na da manyan makamai
  • Ya bayyana haka ne bayan yan ta'adda sun farmaki kauyen Ngoshe inda aka kashe manoma shida da sace wasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume ya shawarci shugaban kasa kan yadda za a magance matsalar tsaro.

Sanata Ali Ndume ya ce dole a dauko sojojin haya domin karar da yan ta'adda da masu garkuwa da mutane da su ka addabi yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Iran vs Isra'ila: Gwamnati ta aika sakon gaggawa ga 'yan Najeriya mazauna Lebanon

Tinubu
Sanata Ndume ya bayar da shawarar dauko sojojin haya kan ta'addanci Hoto: Bola Tinubu/ Sen. Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Sanata Ali Ndume ya bayar da shawarar ne bayan yan ta'adda sun farmaki mazauna Ngoshe a karamar hukumar Gwoza da ke Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu ya nemi taimako daga waje:" Sanata Ndume

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Sanata Ali Ndume ya ce sojojin haya za su iya kakkabe masu tayar da kayar baya a Najeriya matukar aka dauko su.

Ya na wannan batu ne bayan an kashe manoma shida, tare da sace wasu mutum biyar da yan ta'adda su ka yi a karamar hukumar Gwoza da ke Borno.

Gwamnati ta nemi taimako kan ta'addanci

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa kowace gwamnati a fadin duniya ne neman taimakon sojojin haya a wasu wuraren domin magance matsalolinta.

Ya ce idan gwamnatin Najeriya ta dauko hayar irin wadannan, za su shigo da manyan makaman da za su yi maganin Boko haram da sauran bata gari.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Tinubu ya gano dalilin karuwar ta'addanci

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana takaici kan karuwar ayyukan yan ta'adda, lamarin da ya hana jama'a sakewa a kasar su.

Shugaba Tinubu ya ce kudin da ake samowa daga kasashen waje ne ke kara tunzura ayyukan yan ta'adda da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida a yankin Afrika baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.