Matasa Sun Barke da Zanga Zanga a Ofishin INEC, Sun Fadi Bukatunsu

Matasa Sun Barke da Zanga Zanga a Ofishin INEC, Sun Fadi Bukatunsu

  • Matasa masu zanga-zanga sun mamaye ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke birnin Akure a jihar Ondo
  • Masu zanga-zangar sun buƙaci a gaggauta tsige kwamishiniyar hukumar INEC ta jihar Ondo daga kan muƙaminta
  • Sun zarge ta da ɗasawa da ƴaƴan jam'iyyar APC yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar na ranar, 16 ga watan Nuwamban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Matasa sun gudanar da zanga-zanga a ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na jihar Ondo.

Matasan sun buƙaci a gaggauta tsige kwamishiniyar hukumar INEC ta jihar Ondo, Oluwatoyin Babalola daga muƙamin ta.

Matasa sun yi zanga zanga a ofishin INEC a Ondo
Matasa sun yi zanga zanga a ofishin INEC a Ondo Hoto: INEC Nigeria
Asali: Getty Images

Matasa sun mamaye ofishin INEC

Matasan waɗanda suka mamaye ofishin na INEC da ke Akure a ranar Laraba, sun zargi Oluwatoyin Babalola da ɗasawa da da wasu ƴan siyasa gabanin zaɓen gwamnan jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ighodalo: Sabuwar zanga zanga ta ɓarke a hedkwatar hukumar INEC, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar INEC ta sanar da ranar 16 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaɓen gwamna a jihar.

Matasan ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban, sun ce ci gaba da zaman Oluwatoyin Babalola a muƙaminta, zai kawo rashin gaskiya a zaɓen, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.

Wace buƙata suka nema?

Ijanusi Olawale, wanda ya yi magana a madadin masu zanga-zangar, ya yi zargin cewa Oluwatoyin Babalola tana ɗasawa da ƴaƴan jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Ijanusi Olawale, wanda ya zarge ta da zama ƴar jam'iyyar APC, ya ce dole ne ta fice daga hukumar domin ba da damar gudanar da zaɓen gwamna cikin gaskiya da adalci.

Ya roƙi shugaban hukumar INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu da ya sauya mata wurin aiki zuwa wajen jihar yayin da ya buƙaci a naɗa jami'in zaɓe wanda ba zai nuna son kai ba a zaɓen.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi nasara kan APC ana shirin zaben gwamna

Karanta wasu labaran kan INEC

SERAP ta shawarci INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta bukaci hukumar INEC da ta bi umarnin kotu na fara bincike kan zarge-zargen rashawa da magudin zabe da aka tafka a 2023.

SERAP ta buƙaci shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ya tabbatar ya binciki gwamnoni da mataimakansu kan rashawa da laifuffukan zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng