An Harbe Dan Banga yayin Gumurzu da Yan Bindiga, Gari Ya Birkice da Zanga Zanga
- Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kashe wani jagoran yan banga da ya cire tsoro ya tunkare su domin ceto wasu mata
- An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Igbaja a karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya
- Matasan garin Igbaja sun birkice da zanga zanga kan kashe jagoran yan bangar da miyagun suka yi yayin wata arangama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara - Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kashe wani jagoran yan banga mai suna Lukman Bologun a Kwara.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe jagoran yan bangar ne bayan ya fafata da yan bindiga a wani fada da suka yi.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa rundunar yan sanda a jihar Kwara ta tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe jagoran yan banga a Kwara
Masu garkuwa da mutane sun kashe jagoran yan banga mai suna Lukman Bologun da ya yi fada da su.
Marigayin ya jagoranci yan banga ne suka yi musayar wuta da masu garkuwa da mutanen bayan sun sace wasu mata 3 da suka yi.
Matasa sun barke da zanga zanga
Bayan kashe Lukman Bologun, matasan garin Igbaja sun barke da zanga zanga domin nuna bacin rai kan kashe shi.
Sarkin garin, Oba Ahmed Babalola Arepo III ya yi kira ga matasan kan su kwantar da hankali a kan cewa za a tabbatar da kama yan bindigar.
Bayanin yan sanda kan kisan dan banga
Kakakin yan sanda Kwara, ASP Toun Ejire-Adeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya yi Allah wadai da kisan.
Shugaban karamar hukumar Ifelodun, Femi Yusuf ya ziyarci wajen da abin ya faru kuma a yanzu haka jami'an tsaro sun bazama neman yan bindigar.
Iran ta kai hari Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa a ranar Talata aka wayi gari da zafafan hare hare a Tel Aviv, babban birnin kasar Isra'ila.
Kasar Iran ce ta dauki nauyin kai hare haren kuma ta bayyana dalilan da suka sanya ta daukar matakin a kan Isra'ila a wannan lokacin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng