Gwamnatin Tinubu Ta Fara Rabawa Matasa Keke Napep 2000 Marasa Amfani da Fetur

Gwamnatin Tinubu Ta Fara Rabawa Matasa Keke Napep 2000 Marasa Amfani da Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da raba Keke Napep ga matasan kasar nan 2,000 domin sama masu abin yi
  • Daraktan shirin shugaban kasa kan samfurin gas na CNG ya ce an harhada baburan masu tayoyi uku ne a Najeriya
  • Ana rabon Keke Napep din ta hannun ma'aikatar cigaban ma'aikata, kuma an kaddamar da shi a taron murnar yanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da fara rabon Keke Napep mai amfani da gas samfurin CNG domin tallafawa matasan kasar nan.

Ana rabon Keke Napep din ne ta hannun ma'aikatar cigaban ma'aikata, wanda aka kaddamar a babban faretin bikin zagowar ranar samun yancin kai a Abuja.

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Tinubu
Gwamnatin tarayya ta fara raba Keke Napep ga matasa Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa ana sa ran raba baburan masu kafafu uku domin ba matasan da za su rabauta damar dogaro da kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta ba matasa Keke Napep

Jaridar Punch ta wallafa cewa daraktan shirin shugaban kasa kan gas din CNG, Michael Oluwagbemi ya ce shugaban kasa, Bola Tinubu ya cika alkawarin da ya dauka na raba Keke Napep.

Ya ce tun da baburan za su rika amfani da samfurin iskar gas mara gurbata yanayi sosai, za a samu karin arziki da inganta muhalli a fadin kasar nan.

An kera Keke Napep 2000 a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an kera keke napep din da za a raba ga matasan kasar nan a wani kamfani da ke cikin Najeriya, a Shagamu.

Gwamnatin ta kara da cewa an horar da matasa sama da 50,000 a kan yadda za su rika hada da gyara baburan, kuma ana sa ran za a kara horar da wasu.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Bayan lissafo matsaloli, gwamna ya fadi abin da ake bukata daga yan Najeriya

Gwamnati na shirin raba Keke Napep

A wani labarin, mun wallafa cewa karamin Ministan cigaban matasa, Ayodele Olawale ya bayyana shirin gwamnati na raba keke napep.

Ya bayyana cewa matasan da za su rabauta da babura za su rika kashe 20% na abin da su ke kashewa kan fetur, kuma za a samu raguwar kudin mota ga fasinjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.