Tsohon Ministan Sadarwa Ya Rasu? An Samu Karin Bayani kan Jita Jitar

Tsohon Ministan Sadarwa Ya Rasu? An Samu Karin Bayani kan Jita Jitar

  • A kwanakin nan aka yi ta yada labarin cewa wani tsohon Ministan Sadarwa, ya riga mu gidan gaskiya
  • Tajudeen Olanrewaju ya karyata labarin da ake yadawa inda ya ce wasu ne ke neman ganin bayansa haka kawai
  • Hakan ya biyo bayan wata sanarwa da aka fitar inda aka ce tsohon Ministan ya gamu da hatsarin mota

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Tsohon Ministan Sadarwa, Manjo-janar Tajudden Olanrewaju ya yi magana kan jita-jitar mutuwarsa.

Tsohon Ministan ya karyata labarin da ake yadawa cewa ya mutu inda ya ce yana nan da ransa.

Tsohon Minista ya karyata labarin cewa ya mutu
Tsohon Ministan Sadarwa, Tajudden Olanrewaju ya musanta labarin mutuwarsa. Hoto: Tajudden Olanrewaju.
Asali: Facebook

Tsohon Minista ya magantu kan labarin mutuwarsa

Tribune ta ruwaito cewa an yi ta yada mutuwar tsohon Ministan inda aka ce ya gamu da mummunan hatsarin mota.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Bayan lissafo matsaloli, gwamna ya fadi abin da ake bukata daga yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi ta yada mutuwar Tajudden ne wanda tsohon soja ne inda har an sanar da ranar birne shi wanda ya yi matukar firgita tsohon Ministan har ya yi martani.

Olanrewaju ya nuna damuwa inda ya ce hakan wani shiri ne na masu neman ganin bayansa inda ya yi addu'ar ka da Allah ya sa shirin kashe shi ake yi.

Tsohon Ministan ya ce Allah yana kare bayinsa inda ya ce yana nan daram cikin koshin lafiya da kuma walwala.

Olanrewaju ya tsorata da zargin hallaka shi

"Wannan wani shiri ne na wasu shaidanu da ke neman kashe ni, akwai matsala a cikin sanarwar da ake yadawa."
"Ina fatan wannan ba wata makarkashiya ba ce na kawo mani farmaki, Allah yana kare bayinsa ta kowace hanya, ina nan cikin koshin lafiya."

- Tajudden Olanrewaju

Tsohon Minista ya ba yan siyasa shawara

Kara karanta wannan

'Babu abin da ya dame mu': Turji ya fito ya cika baki kan kisan Halilu Sububu

Kun ji cewa tsohon Ministan shari'a a mulkin shugaba Olusegun Obasanjo ya shawarci yan siyasa kan magudin zabe a Najeriya.

Kanu Agabi ya ce babu yadda za a yi tun daga zabukan tsaida gwani a yi magudi kuma a yi tsammani taimakon Ubangiji.

Lauyan ya koka kan yadda shugabannin yanzu da yan siyasa suka koma bautar neman gidaje da kudi da kuma mata a rayuwarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.