Sarautar Kano: Gwamnatin Abba Ta Koma Kotu da Aminu Ado, An Sa Ranar Hukunci

Sarautar Kano: Gwamnatin Abba Ta Koma Kotu da Aminu Ado, An Sa Ranar Hukunci

  • Babbar kotun Kano ta zabi ranar 10 ga watan Oktoba, 2024 domin yanke hukunci a ƙarar da aka nemi dakatar da gyara fadar Nassarawa
  • Gwamnatin Kano ta buƙaci kotun ta hana Sarki na 15, Aminu Ado Bayero aiwatar da shirinsa na gyaran fadar da yake ciki yanzu
  • Kotun ƙarƙashin jagarancin Mai shari'a Dije Aboki ta shirya yanke hukunci kan buƙatar lauyan gwamnati a zamanta na yau Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Babbar kotun jihar Kano ta shirya yanke hukunci kan batun gyaran karamar fadar sarkin Kano da ke Nassarawa.

Kotun ta zaɓi ranar 10 ga watan Oktoba, 2024 domin yanke hukunci a karar da aka nemi takawa sarki na 15, Aminu Ado Bayero burki a shirinsa na gyara ƙaramar fadar.

Kara karanta wannan

Ana fama da wahala, gwamna ya rabawa manyan sarakunan Arewa 4 motocin alfarma

Gwamna Abba da Aminu Ado Bayero.
Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan gyaram fadar da Aminu Ado ke ciki Hoto: Abba Kabir Yusuf, Aminu Ado Bayero
Asali: Twitter

Dalilin gwamnatin Abba na kai karar Aminu

Leadership ta ruwaito cewa waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf, Antoni Janar da masarautar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Abba ta bukaci kotun ta hana gyaran ƙaramar faɗar da ke Nasarawa domin riƙe tsarin ginin da kayan tarihin da ke cikin fadar.

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ne kaɗai wanda ake tuhuma a ƙarar saboda shirinsa na rushe fadar da yake ciki domin yi mata kwaskwarima.

Kano: Yadda zaman kotun ya kasance

A zaman kotun na yau Laraba karkashin Mai Shari'a Dije Aboki, lauyan gwamnati ya ce har yanzun babu wakilci daga wanda ake ƙara.

Don haka lauyan ya bukaci kotu ta hana wanda ake tuhuma sake ginawa, rushewa ko canza fasalin karamar fadar.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

Kotun Kano ta ɗauki mataki

Bayan sauraron ɓangaren gwamnati, Mai Shari'a Dije Aboki wadɗa ita ce shugabar alkalan Kano ta ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba domin yanke hukunci.

Ta kuma ba da umarnin cewa a liƙa yadda zaman shari'ar ya kasance a allon sanarwa na babbar kotun jihar, kamar yadda PM News ta rahoto.

Sanusi II ya yi naɗe-naɗen sarauta

A wani rahoton kuma sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II zai yi nade-naden sarauta a jihar Kano, kusan wannan shi ne mafi girma bayan dawowarsa karaga.

Bayanan da aka samu sun nuna an gabatar da canje-canje 14 wadanda mai martaba Muhammadu Sanusi II ya amince da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262