Duk da Gazawar Tinubu, Gwamna Zai Fara Biyan Albashin N70,000 a Watan Oktoba

Duk da Gazawar Tinubu, Gwamna Zai Fara Biyan Albashin N70,000 a Watan Oktoba

  • Yayin da rayuwa ke kara tsada duk kwanan duniya a Najeriya, Gwamna Charles Soludo zai biya sabon albashi
  • Gwamna Soludo ya amince da fara biyan sabon mafi karancin albashin N70,000 a karshen wannan watan Oktoba
  • Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne domin saukakawa ma'aikata da kuma samar da ilimi kyauta ga daliban sakandare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya shirya biyan mafi karancin albashi na N70,000.

Soludo ya yi alkawarin fara biyan sabon albashin a karshen wannan wata da muke ciki na Oktoba.

Gwamna ya shirya biyan mafi karancin albashin N70,000
Gwamna Charles Soludo zai fara biyan mafi karancin albashi a karshen watan Oktoba. Hoto: Charles Soludo.
Asali: Facebook

Gwamna Soludo zai fara biyan albashin N70,000

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron cikan Najeriya shekaru 64 da samun yancin kai, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Soludo ya ce zai ba da mafi karancin albashi a karshen watan nan da kuma ilimi kyauta domin taba kowane bangare na al'umma.

Ya ce ya dauki wannan mataki ne duba da halin da al'umma ke ciki na matsin rayuwa da tattalin arziki.

Soludo ya kuma sanar da cewa za a fara ba manyan dalibai da ke makarantar sakandare ilimi kyauta, cewar rahoton Punch.

Gwamna ya ba tabbaci kan halin kunci

"Mun taru a nan domin bikin cika Najeriya shekaru 64 da samun yancin kai duk da kalubalen da muke fuskanta."
"Kalubalen da yawa amma duk da haka ina mai tabbatar muku da cewa komai zai daidata, ina hango jin dadi a gaba."

Charles Soludo

Hakan na zuwa ne yayin da rahotanni suka tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta fara biyan mafi karancin albashi inda wasu ma'aikata suka musanta.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

Tinubu ya kasafta sabon albashin N70,000

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da jadawalin yadda kowane ma'aikaci zai samu a sabon mafi ƙarancin albashin da aka kawo.

An kasafta tsarin yadda ma'aikatan gwamnati za mu samu albashi har na tsawon shekara bayan karin kudin da aka yi masu.

Hakan na zuwa bayan rahotanni sun tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashi a ranar Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.