An Shiga Tashin Hankali a Benue, 'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji da Farar hula

An Shiga Tashin Hankali a Benue, 'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji da Farar hula

  • Wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai sabon hari kauyen Eguma da ke karamar hukumar Agatu a jihar Benuwai
  • An rahoto cewa 'yan ta'addan sun kashe sojoji biyu, hakimin Eguma da kuma wasu mutane shida a harin da suka kai ranar Talata
  • Wani tsohon dan majalisar dokokin da ya wakilci yankin karamar karamar hukumar Agatu, Audu Sule ya ba da rahoton farmakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benuwai - An shiga tashin hankali a kauyen Eguma da ke karamar hukumar Agatu, jihar Benuwai bayan wasu 'yan bindiga sun kashe sojoji da farar hula.

'Yan bindigar da ake zargin makiyaya ne sun kashe sojoji biyu da mutanen kauyen bakwai, ciki har da hakimi a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 7 daga jawabin Tinubu na ranar samun 'yanci

'Yan bindiga sun kashe sojoji da fararen hula a jihar Benuwai
'Yan bindiga sun halaka sojoji da fararen hula a harin da suka kai Benuwai. Hoto: AFP
Asali: Getty Images

Wani tsohon dan majalisa, wanda ya wakilci karamar hukumar a majalisar dokokin jihar Benue tsakanin 2011 zuwa 2019 ya shaidawa Channels TV labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kai hari a Benuwai

A tattaunawa ta wayar tarho, Hon. Audu Sule, ya ce makiyayan da ake zargi sun shigo kauyen Eguma ne da karfe 3:00 na rana inda suka fara kashe mutane.

A cewar Hon. Sule, jami’an soji da ke a kauyensu na Ogwule mai tazarar ‘yan mitoci daga inda aka kai harin, sun aikawa kauyen Eguma dauki cikin gaggawa.

Sai ya ce makiyayan da ake zargi sun kashe biyu daga cikin sojojin tare da hakimin kauyen Eguma da wasu mutane shida, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa tara.

An kashe sojoji 2 da fararen hula

Hon. Sule ya bayyana cewa, harin shi ne na hudu da aka kai a kauyukan Eguma da Ogwule a cikin wata daya, inda ya koka da irin barazanar tsaro da al’ummarsa ke fuskanta a kullum.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Zamfara, wani direban mota ya kashe mutane 6 ƴan gida 1

Ya kara da cewa, kai daukin da sojoji suka yi ya sa an yi musayar wuta da 'yan ta'addan wadanda daga bisani suka tsere bayan sun kashe mutane tara, ciki har da sojoji biyu.

Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Sewuese Anene, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu wani bayani kan kisan ko harin da aka kai Agatu ba.

'Yan bindiga sun kashe mutane 30

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun halaka mutane 30 a kauyen Ayati da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benuwai.

Mazauna yankin sun bayyana cewa da yiwuwar waɗanda aka kashe a harin su haura 50 saboda har yanzun ana kan binciken gawarwaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.