Najeriya @64: Muhimman Abubuwa 5 da Tinubu Zai Yi Domin Ceto Kasa a Halin Kunci

Najeriya @64: Muhimman Abubuwa 5 da Tinubu Zai Yi Domin Ceto Kasa a Halin Kunci

Yayin da aka gudanar da bikin cika shekaru 64 da Najeriya ta samun yancin kai, akwai kalubale da dama da ke gaban shugabanni.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Tsohon dan takarar Sanatan SDP a Abuja a zaben 2023, Olanrewaju Osho ya koka kan yadda komai ya lalace a Najeriya.

Abin da Tinubu zai yi domin inganta Najeriya
Muhimman abubuwa 5 da Bola Tinubu zai yi domin kawo sauyi a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Osho ya lissafo hanyoyi biyar da jaridar TheCable ta wallafa da shugaba Bola Tinubu zai bi domin dawo da martabar kasar.

Legit Hausa ta duba abubuwan da Osho ya lissafo domin inganta Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Nada kwararru a mukami

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Osho ya ce idan har Tinubu na son gyara Najeriya dole ya nada mutane masu kwarewa mukamai.

Ya ce tabbas hakan zai saka ya yi bakin jini a wurin yan jam'iyyarsa amma kuma hakan shi ne mafita domin kawo sauyi a kasa.

2. Gudun aikata kuskure

Babban kuskuren da Bola Tinubu ya yi shi ne cire tallafin mai da kuma tsarin gudanar da Naira.

Osho ya ce duk da Tinubu ya yi hakan domin kawo sauyi amma ya kamata a kawo tsare-tsare kafin aiwatarwa.

3. Damawa da yan kasa

Dole idan ana so gwamnati ta samu cigaba a rika damawa da yan kasa wurin kawo sababbin tsare-tsare musamman da ya shafe su kai tsaye tare da jin ra'ayinsu.

4. Yaki da cin hanci

Duk kasar da ba ta yaki cin hanci ba dole ta samu koma-baya ta ɓangarori da dama.

Dole Tinubu ya yaki cin hanci tun daga mukarrabansa da ke sama domin dakile matsalar har zuwa kasa.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Abin da Tinubu ya fada game da halin kunci, ya roki yan kasa

5. Almubazzaranci da kudin gwamnati

Dole gwamnati ta dakile yawan almubazzaranci da ake yi da kudin al'umma wanda ke kawo cikas ga cigaban ƙasa.

Mafi yawan yan siyasa suna ɗaukar kudin gwamnati a matsayin na banza wanda hakan ke sanya gaba tsakanin gwamnatin da talakawa.

Halin kunci: Tinubu ya roki yan Najeriya

Kun ji cewa, shugaba Bola Tinubu ya sake yin magana kan halin kunci da yan Najeriya ke ciki a yanzu.

Tinubu ya bukaci hadin kan yan kasa domin kawo sauyi da tabbatar da rage tsadar abinci da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.