Ana Fargabar 'Yan Maulidi 150 Sun Rasu bayan Haɗarin Jirgin Ruwa

Ana Fargabar 'Yan Maulidi 150 Sun Rasu bayan Haɗarin Jirgin Ruwa

  • Yan Maulidi kimanin 300 sun samu mummunan haɗarin jirgin ruwa a yankin Gbajibo a karamar hukumar Mokwa a jihar Neja
  • Rahotanni sun nuna cewa ana cikin fargaba kan cewa mutane sama da 150 suka rigamu gidan gaskiya bayan jirgin ruwan ya kife
  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta ce a yanzu haka ana ƙoƙarin ceto wadanda haɗarin da ya ritsa da su kuma an ceto da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Rahotanni da suka fito daga jihar Neja na nuni da cewa an samu mummunan hadarin jirgin ruwa.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja ta tabbatar da cewa kimanin mutane 300 ne suka kife a kwale-kwalen.

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Jirgin Ruwa
Yan Maulidi 300 sun yi hadari. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ana fargabar cewa mutane 150 sun rigamu gidan gaskiya a hadarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Maulidi sun yi hadarin jirgi a Neja

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a daren Talata, 1 ga watan Oktoba aka samu mummunan haɗarin jirgin ruwa a Neja.

An ruwaito cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na dare a karamar hukumar Mokwa yayin da mutanen ke tafiya taron Maulidi.

Ana fargabar yan Maulidi 150 sun bace

An ruwaito cewa sama da mutane 300 suka shiga jirgin ruwan domin tafiya Maulidi a wani kauye.

Amma bayan hadarin an iya ceto mutane 150 kawai wanda hakan yasa ake cikin fargabar mutuwar sauran mutanen.

Bayani SNEMA kan hadarin Maulidi

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (SNEMA), Alhaji Abdullahi Baba Arah ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

Sai dai Alhaji Abdullahi Baba Arah ya ce a yanzu haka ana cigaba da ƙoƙarin neman mutanen da ba a gansu ba.

'Yan Maulidi sun yi hadari a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa an samu mummunan haɗarin mota da ya ritsa da yan Maulidi a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa.

Bayanai sun nuna cewa matukin wata mota ne ya haura kan mutane suna tafiya yayin bikin Maulidi kuma ya kashe wasu daga cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng