Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Wani Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Jihar APC

Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Wani Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Jihar APC

  • Wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya afku ya yi ajalin mutum huɗu a yankin Ikorodu da ke jihar Legas ranar Litinin
  • Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar (LASWA) ta ce jami'ai sun yi nasarar ceto fasinjoji 11 na jirgin amma ba su gano abinda ya haddasa haɗarin ba
  • A halin yanzun jami'an LASWA sun mika gawarwakin da aka gano da waɗanda suka tsira ga hukumar LASEMA

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Aƙalla mutum huɗu ne aka tabbatar sun riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya auku a yankin Ikorodu, jihar Legas.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa jirgin ruwan ya taso ne daga Addax jetty a jihar Legas a hanyarsa ta zuwa Ebute Ipakodo a Ikorodu lokacin da haɗarin ya afku.

Kara karanta wannan

Dandutse: Ƴan bindiga sun kashe babban soja da wasu jami'ai biyu, sun tafka ɓarna kan bayin Allah

Jirgin ruwa ya yi ajalin mutane 4 a jihar Legas.
Mutum 4 Sun Kwanta Dama a Wani Hadarin Jirgin Ruwa da Ya Afku a Jihr Legas Hoto: leadership
Asali: Getty Images

An gano cewa jirgin ruwan ya kife ne a daidai Ibeshe/Ikorodu da misalin ƙarfe 7:17 na daren ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun hukumar kula da harkokin ruwa ta jihar Legas (LASWA), Wuraola Alake, ta tabbatar da faruwar haɗarin a wata sanarwa ranar Talata.

Ta bayyana cewa tuni jami'anta suka tsamo jirgin ruwan da ya nutse kuma sun gano gawarwakin mutane 3 tare da ceto fasinjoji 11 da ransu, rahoton Vanguard.

Mutum nawa aka tabbatar da sun mutu a hatsarin?

Amma da take ƙarin bayani kan hatsarin bayan haka, Alake ta ce jami'an hukumar LASWA sun tsamo ƙarin gawa ɗaya a wurin da lamarin ya afku.

Ta ce:

"Har yanzu muna bincike don gano ainihin abinda ya jawo haɗarin, yayin da wasu daga cikin fasinjojin da aka ceto suka musanta ikirarin cewa jirgin ruwan da ya yi hatsarin ya shiga tsere ne da wasu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da dakarun sojoji sun yi wa ƴan bindiga rubdugu, sun samu gagarumar nasara a Arewa

"An tabbatar da ceto fasinjoji 11 a raye, yayin da aka mika wadanda suka mutu ga hukumar ba da agajin gaggawa ta Legas LASEMA da hukumar kula da lafiyar muhalli ta jihar (SEHMU).
"Fasinjojin ba su cike bayanansu a takarda gabanin hawa jirgin a tashar Addax Jetty, amma bayan ceto su, 9 daga cikin 11 sun cike takardar, biyu kuma sun yi kunnen ƙashi."

Matashi ya halaka mahaifinsa a Jos

A wani rahoton kuma Yan sanda sun kama wani matashi ɗan shekara 29 a duniya bisa zargin ya halaka mahaifinsa a Jos, babban birnin jihar Filato

Rahoto ya nuna matashin mai suna, Joseph Yakubu, ya ɗauki taɓarya ya maka wa mahaifinsa a kai bayan sun samu wani ɗan saɓani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel