Garambawul: An Bukaci Tinubu Ya Nada El Rufai da Wasu Mutum 4 Ministoci
- An buƙaci Bola Tinubu da ya naɗa Nasir El-Rufai a matsayin minista a yayin da yake shirin yin garambawul a majalisar FEC
- Ƙungiyar Mandate Protection Vanguard (MPV) ta ba da wannan shawarar ne a cikin wata sanarwa da shugabanta ya fitar
- A cewar ƙungiyar, Shehu Sani da wasu mutane uku ya kamata a ba su muƙamai domin su yi wa ƙasa hidima ƙarƙashin Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar Mandate Protection Vanguard (MPV) ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin muƙamin minista.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci Tinubu da ya naɗa wasu gogaggun mutane a matsayin ministoci a shirin da yake yi na yiwa majalisar ministocinsa garambawul.
An shawarci Tinubu kan naɗa ministoci
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƙungiyar MPV ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da shugabanta Kwamared Gbenga Soloki ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar ta jaddada cewa ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu ta fuskar tattalin arziki na buƙatar ministoci waɗanda suka ƙware sosai ta fuskar tattalin arziƙi.
Ta bayyana cewa ya kamata su kasance waɗanda za su iya samar da sakamakon da ake buƙata da kuma yaɗa manufofin gwamnati, rahoton Politics Nigeria ya tabbatar.
Ga jerin mutanen da ƙungiyar ta buƙaci a naɗa ministoci:
1. Malam Nasir El Rufa'i
Ƙungiyar MPV ta bayyana El-Rufai a matsayin gogaggen ɗan siyasa wanda ya yi digiri na biyu a fannin harkokin gwamnati daga jami’ar Harvard.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya taɓa zama Darakta Janar na hukumar BPE da ministan birnin tarayya Abuja.
2. Sanata Shehu Sani
An bayyana tsohon Sanatan a matsayin wanda ya kasance mai kishin dimokuraɗiyya kuma mai fafutukar tabbatar da mulkin dimokradiyya a Najeriya.
3. Farfesa Bart Nnaji
Ƙungiyar ta ce Farfesa Bart Nnaji ƙwararre ne a bangaren gudanarwa kuma farfesa a fannin Injiniyan lantarki.
Ta bayyana cewa yana da gogewa a matsayin tsohon ministan makamashi kuma tsohon shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC).
4. Sanata Adeleke Mamora
A cewar ƙungiyar, Adeleke Mamora ƙwararren likita ne, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Legas, kuma tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari.
5. Ojo Samuel Olukunle
Ƙungiyar ta ce Ojo Samuel Olakunle wanda tsohon babban sakatare ne kuma tsohon shugaban ma'aikatan gwamnan Legas, ya ƙware ta fannin manufofin gwamnati, kuɗi da kasafin kuɗi.
Shawarwarin ƙungiyar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa za a yiwa majalisar ministoci garambawul.
Jigon APC ya kare Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya yi magana kan salon mulkin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Jigon na APC ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara ba shugaba Tinubu lokaci domin shawo kan matsalar tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng