Murnar Samun 'Yanci: Gambo Sawaba da Fitattun Mata 2 da Su ka Jijjiga Siyasar Najeriya

Murnar Samun 'Yanci: Gambo Sawaba da Fitattun Mata 2 da Su ka Jijjiga Siyasar Najeriya

Duk da cewa tarihi ya nuna cewa a kasashe masu tasowa kamar Najeriya, mata na fuskantar matsaloli da dama wanda ke hana su bada gudunmawa ta fuskar shugabanci da kawo ayyukan ci gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Amma hakan bai hana wasu fitattaun mata bayar da ta su gudunmawar a siyasar kasar nan ba, musamman bayan samun yancin kai a 1960.

Legit ta tattaro bayanan wasu muhimman mata uku da siyasar kasar nan ba za ta manta da su ba a kasa.

Women
Gambo Sawaba da wasu mata da su ka yi fafutaka a siyasar Najeriya Hoto: Alhassan M. Wokili/awomantoknow/Funmilayo Ransome kuti
Asali: UGC

1. Yar gwagwarmaya, Hajiya Gambo Sawaba

Hajiya Gambo Sawaba ita ce mace daya tilo da ta shahara a siyasar Arewacin Najeriya a tun daga lokacin samun ‘yancin kai har zuwa shekarar 1990.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haife ta ranar 15 Fabrairu, 1933 a Lavun, da ke jihar Neja, kuma ta fuskanci kalubalen rayuwa da ya sauya tunaninta ciki har da zaman kurkuku na shekaru 16, kamar yadda Aljazeera ta wallafa.

Ta kasance 'yar jam'iyyar adawa a wancan lokacin watau NEPU, inda suka yi gwagwarmayar siyasa tare da marigayi Malam Aminu Kano, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Gambo Sawaba ba ta taba rike wani mukami na gwamnati ba, amma ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan yan kasa da faftukar kwatar hakkin talakawa da yakar nuna wariya ga mata a yankin.

2. Mace yar siyasa: Funmilayo Ransome kuti

An haife Funmilayo Ransome-Kuti a 25 Oktoba, 1900. Ta na daga cikin matan da suka taka rawar gani a fagen siyasar kasar nan, don ana iya cewa ita ce mace ta farko da ta fara kafa jam'iyyar siyasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Bayan lissafo matsaloli, gwamna ya fadi abin da ake bukata daga yan Najeriya

Ta na cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar National Council of Nigeria and the Cameroons, (NCNC) a shekarar 1944 inda daga baya ta tsaya takarar ‘yar majalisa, amma ba ta yi nasara ba.

3. Cif Magaret Ekpo, mai fafutukar zabe

Margaret Ekpo da aka haife ta a 21 Disamba, 1914 ta kasance shugabar mata kuma yar majalisar dokoki da ta bayar da babbar gudunmwa a fagen siyasar Najeriya tun kafin ta samu yancin kai.

Tana cikin manyan mambobin jam'iyyar NCNC kuma ta taba riƙe mukamin mataimakiyar shugabar kungiyar mata ta jam'iyyar.

Cif Margaret ta kasance mai fafutukar ganin hadin kan yan Najeriya da tabbatar da samun yancin mata musamman a bangaren siyasa.

Ta riƙe muƙamin shugabar mata a jam'iyyar inda ta tsaya tsayin daka don ƙwatar wa mata yancinsu na yin zabe da tsayawa takara.

Tafiye tafiye matar Tinubu ya ci N701m

A baya mun wallafa cewa yawan tafiye-tafiye da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ya lakume makudan kudi da ya kai Naira miliyan 701 a watanni uku kacal.

Kara karanta wannan

Kungiyoyi a Kaduna sun barranta da zanga zangar 1 ga watan Oktoba

An gano cewa gwamnatin ta biya Naira miliyan 700,707,532 a tsawon watanni uku, saboda tafiye-tafiyen da ta yi zuwa kasashe biyar, ciki har da kasashe biyu na Afrika.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.