Funmi Ransome-Kuti: Mace ta samu shiga cikin sunayen da aka yi wa tashoshin jirgin kasa

Funmi Ransome-Kuti: Mace ta samu shiga cikin sunayen da aka yi wa tashoshin jirgin kasa

A ranar Litinin, 27 ga watan Yuli, 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya sa sunayen tashoshin jirgin kasa bayan wasu ‘yan Najeriya da su ka cancanta da karramawa.

A cikin wannan jerin manyan kasa da aka karrama, mace guda kacal aka samu. Wannan mace kuwa ita ce Funmilayo Ransome-Kuti wanda aka fi sani da Funmilayo Anikulapo-Kuti.

Madam Funmilayo Anikulapo-Kuti MON ta rasu ne a 1978 ta na mai shekara kusan 78 da haihuwa. Marigayiyar ita ce macen farko da ta halarci makarantar Abeokuta Grammar School.

Funmilayo Anikulapo-Kuti ta yi karatu a Ogun da kasar Ingila, ta kuma yi aiki a matsayin malamar makaranta, sannan ta yi gwagwarmaya wajen karbowa mata hakki a lokacinta.

Daga cikin ‘ya ‘yanta akwai shararren mawakin nan Fela Kuti, da kuma Beko Ransome-Kuti. Sauran ‘ya ‘yanta su ne: Olikoye Ransome-Kuti, da Dolupo Ransome-Kuti.

Mutane 23 shugaban kasa Buhari ya karrama, daga cikinsu akwai tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan; jagoran APC, Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

KU KARANTA: PDP ta soki Buhari a kan tafiyar da ta yi zuwa Mali

Funmi Ransome-Kuti: Mace ta samu shiga cikin sunayen da aka yi wa tashoshin jirgin kasa
Marigayiya Funmilayo Anikulapo-Kuti da iyalinta
Asali: UGC

A jerin akwai karin wasu tsofaffin gwamnan Legas Babatunde Fashola da Lateef Jakande. Farfesa Wole Soyinka da tsohon mataimakin shugaban kasa, Dr. Alex Ekwueme.

Jaridar The Cable ta ce karancin matan da aka samu bai yi wa jama’a dadi ba. Wasu sun yi tunanin za a karrama irinsu Dr Stella Adadevoh wanda ta mutu wajen yaki da cutar Ebola a 2014.

Sanata Shehu Sani ya bada shawarar a sa sunan tashar jirgin Kaduna bayan Tolulope Arotile, macen da ta zama matukiyar jirgin yakin farko a cikin sojoji wanda ta mutu kwanaki.

A halin yanzu dai kason matan da ke cikin majalisar ministocin shugaba Buhari ba su kai kashi 20% ba. Haka zalika daga cikin manyan hadimansa babu mata sosai.

Abin da ya bada mamaki shi ne a wannan jeri babu tsohon shugaban kasa Obasanjo wanda ya yi mulki a lokacin soji da farar hula, kuma ya fara wasu daga cikin aikin dogo a gwamnatinsa.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki ya yi murna da gwamnati ta zabi ta karrama shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng