Gambo Sawaba: Abokiyar siyasar Malam Aminu Kano, wacce tayi zaman kurkurku sau 16

Gambo Sawaba: Abokiyar siyasar Malam Aminu Kano, wacce tayi zaman kurkurku sau 16

Duk da karancin ilimin ta, da kuma kasancewa ta fito daga yankin Arewa, hakan bai hana Hajiya Hajara Gambo Sawaba fafatawa ba wajen ganin ta bada gudunmuwa a kokarin samar ma Najeriya yanci kai, tare da kwatarma mata da talakawa hakkokinsu ba.

An haifi Hajara Gambo Sawaba ne a ranar 15 ga watan Feburairun shekara ta 1933, daga tsatson Malama Fatima mahaifiyarta da wani mutumin kasar Ghana, Theophilus Wilcox Amarteifo, wanda daga bisan ya musulunta yana koma Isa.

KU KARANTA: Menene dalilin da yasa aka kashe Ahmadu Bello Sardauna?

Yar fafutukar ta samu suna Gambo ne sakamakon an haife bayan yan biyu, inda ta samu sunan Sawaba daga wani fitaccen dan NEPU dake garin Zaria, Malam Gambo wanda ya rada mata sunan Sawaba.

Gambo Sawaba: Abokiyar siyasar Malam Aminu Kano, wacce tayi zaman kurkurku sau 16
Gambo Sawaba

Tana yar shekara 16 aka yi mata auren fari, inda ta auri mijinta na fari, Abubakar Garba Bello, wani tsohon Soja daya fafata a takin duniya na II, sai dai gab da haihuwarta na fari, inda ta samu Bilkisu, tsohon Soja Abubakar ya tsere. Bayan nan ta auri wani Hamisu Gusau, sai dai auren bai yi dadi ba, inda har dambe suke yi , shima bayan mutuwar auren, ta sake yin aure guda 2.

Sawaba ta zamo yar bakar jam’iyyar NEPU, wanda shine jam’iyyar adawa a wancan zamani, jam’iyyar Malam Aminu Kano, tun tana shekara 17, inda aka nada ta shugaban mata na NEPU reshen unguwar Sabon Gari.

A kokarinta na gogewa a harkar siyasa, Gambo Sawaba ta tafi har wajen Funmilayo Ransome Kuti, Uwar shahararriyar mawakin nan Fela Kuti, a garin Abekuta, inda kara fahimtar yancin mata da matsayin haraji.

Fafutukar Gambo Sawaba ya tattara ne akan yaki da aurar da kananan yara, bautar da mutane, ilimin boko ga yaya mata, wanda hakan ya sanya ta shiga gidan yari har sau 16.

A zamanin jamhuriya na farko ne Gambo Sawaba ta zamo shugaban matan jam’iyyar NEPU, inda a zamanin mulkin Shagari kuma tayi jam’iyyar GNPP.

Gambo Sawaba ta rasu tana da shekaru 71, a ranar 14 ga watan Oktobar 2001a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello, ta rasu ta bar ya mace daya rak, Bilkisu. A yanzu haka akwai asibiti a Zaria da aka sanya ma suna Gambo Sawaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng