Najeriya @64: Tinubu Ya Ba Akpabio, Barau da Wasu Mutum 3 Lambar Yabo Ta Kasa

Najeriya @64: Tinubu Ya Ba Akpabio, Barau da Wasu Mutum 3 Lambar Yabo Ta Kasa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da lambobin yabo na ƙasa domin murnar cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai
  • Shugaba Tinubu ya karrama shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da lambar yabo ta ƙasa ta GCON a ranar 1 ga Oktoba
  • Alƙalin alƙalan Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun da Sanata Barau Jibrin na daga cikin waɗanda suka samu lambobin yabon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da lambar yabo ta ƙasa.

Shugaban ƙasan ya kuma karrama alƙalin alƙalan Najeriya (CJN), Kudirat Kekere-Ekun da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau.

Tinubu ya karrama Akpabio
Tinubu ya ba da lambobin yabo na kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Godswill Obot Akpabio, Kudirat Kekere-Ekun
Asali: Facebook

Tinubu ya ba da lambobin yabo na ƙasa

Kara karanta wannan

Ranar ƴanci: Shugaba Tinubu ya yi magana kan farashin kayan abinci, ya faɗi mafita

Haka kuma shugaban ƙasan ya karrama shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya yi domin murnar zagayowar ranar samun ƴancin kan Najeriya a ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024, wanda hadiminsa Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

"An ba shugaban majalisar dattawa da alƙalin alkalan Najeriya lambar yabo ta Grand Commander of the Order of Niger (GCON)"
"Mataimakin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai sun samu lambar yabo ta Order of the Federal Republic (CFR), yayin da mataimakin kakakin majalisar wakilai ya samu lambar yabo ta Commander of The Order of Niger (CON)."

- Bola Tinubu

Jerin waɗanda Tinubu ya ba lambar yabo

  • Godswill Akpabio - Grand Commander of the Order of Niger (GCON)
  • Kudirat Kekere-Ekun - Grand Commander of the Order of Niger (GCON)
  • Barau Jibrin - Order of the Federal Republic (CFR)
  • Tajudeen Abbas - Order of the Federal Republic (CFR)
  • Benjamin Kalu - Commander of the Order of Niger (CON)

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yancin kai: Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya, an samu bayanai

Shugaba Bola Tinubu ya tuna da matasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa za a gudanar da gagarumin taron matasa na kasa inda za a tattauna da masu ruwa da tsaki.

A jawabinsa na ranar samun yanci a safiyar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024, shugaban ƙasan ya ce za a duba duk wasu matsaloli da kalubale da matasan kasar nan ke fuskanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng