Abuja: 'Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga Zanga, An Harba Barkonon Tsohuwa

Abuja: 'Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga Zanga, An Harba Barkonon Tsohuwa

  • Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zanga a Abuja sun gamu da cikas yayin da 'yan sanda suka rika jefa masu barkonon tsohuwa
  • A ranar Talata, 1 ga watan Oktoba ne matasa suka fara gudanar da zanga zangar nuna adawa da tsadar fetur, kayan abinci da na masarufi
  • Damilare Adenola, daraktan gangamin Take It Back ya ce harbawa matasan barkonon tsohuwa ba zai hana su gudanar da zanga zangar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jami’an ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan gungun masu zanga-zanga a unguwar kasuwar Utako da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Matasa sun taru ne a kasuwar da safiyar Talata, domin gudanar da zanga zangar 1 ga Oktoba, a lokacin da ‘yan sanda suka jefa masu barkon tsohuwar.

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Abin da ke faruwa a Kano bayan fara zanga zanga a wasu sassan Najeriya

'Yan sanda sun watsawa masu zanga zangar 1 ga Oktoba barkonon tsohuwa a Abuja
Masu zanga zanga sun tarwatse a Abuja bayan 'yan sanda sun jefa masu barkonon tsohuwa. Hoto: KOLA SULAIMON
Asali: Getty Images

Zanga zanga ta kankama a Najeriya

Damilare Adenola, daraktan gangami na Take It Back, ya shaidawa The Cable cewa matasan za su sake haduwa domin ci gaba da zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kungiyoyin fararen hula (CSOs) ne suka shirya zanga-zangar a karkashin fafutukar kawo karshen gurbatacciyar gwamnati a kasar nan.

A ranar 1 ga watan Oktoba ne aka fara zanga zangar a Legas da Abuja, inji rahoton Channels TV.

Ana zanga zanga kan tsadar rayuwa

Matasan dai sun ce an shirya zanga-zangar ne domin adawa da hauhawar farashin man fetur, tsadar kayan abinci da kuma illar hauhawar farashin kayayyaki ga rayuwar talaka.

Zanga-zangar ta zo daidai da bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun 'yancin kai, kuma wani mataki ne na ci gaban zanga zangar watan Agusta da aka yi.

Duba wasu labarai kan zanga zanga:

Kara karanta wannan

Oktoba: Zanga zanga ta barke ana tsaka da bikin ranar yanci

KAI TSAYE: Yadda zanga zangar 1 ga Oktoba ke gudana a Najeriya

Zanga zanga ta barke ana tsaka da bikin murnar samun 'yancin Najeriya

Kungiyoyin Arewa sun amsa kiran fitowa zanga zangar 1 ga Oktoba

Kungiya ta nemi a kauracewa zanga zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar matasa a Kaduna (CCC) ta yi kira ga al'ummar jihar da su kauracewa zanga zangar 1 ga watan Oktoba da aka shirya yi.

A cewar kungiyar, zanga-zangar da aka yi a watan Agusta ba ta haifar da da mai ido ba domin haka ne take tsoron ka da ita ma wannan ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.