Najeriya @64: Ana Murnar Samun Ƴanci, Gwamna Ya Ƴanta Fursunoni a Najeriya

Najeriya @64: Ana Murnar Samun Ƴanci, Gwamna Ya Ƴanta Fursunoni a Najeriya

  • Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya 'yanta fursunoni biyar a ranar murnar cika shekaru 64 da samun 'yancin Najeriya
  • Gwamnan ya kuma tabbatarwa al'ummar Filato aniyarsa ta samar da tsare-tsare da za su saukaka masu wahalhalun rayuwa
  • Barista Mutfwang ya kuma daukarwa mutanen Filato alkawarin yin duk mai yiwuwa domin kawo karshen matsalolin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang ya yiwa fursunoni biyar da ke zaman gidan yari daban-daban afuwa.

An rahoto cewa an yafewa fursunonin ne bayan da suka nuna kyakykyawan halaye na tsawon shekaru a cikin gidan yarin.

Gwamnan Filato ya yi jawabin kai tsaye a ranar 'yancin Najeriya
Gwamnan Filato ya yi afuwa ga fursunoni a ranar murnar 'yancin kan Najeriya. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Gwamna Caleb Mutfwang ya 'yanta fursunoni

Karamcin da Gwamna Mutfwang ya nuna ya yi daidai da ikon jinkai da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 7 daga jawabin Tinubu na ranar samun 'yanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabin kai tsaye da ya yi ga al'ummar jiharsa kan bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai a ranar Talata.

A cewarsa, Najeriya a cikin shekaru 64 ta fuskanci nasarori da kalubale yayin da ake ci gaba da gwada hadin kan kasar ta hanyar siyasa, tattalin arziki da zamantakewa.

Gwamna lallashi 'yan Filato

Gwamna Mutfwang wanda ya amince da matsalolin rayuwa da jama'a ke fuskanta, ya kuma tabbatar da aniyarsa ta samar da mafita mai dorewa da za ta kawo sauki ga 'yan jiharsa.

“A halin yanzu muna aiki kan manufofi da tsare-tsare a sassa da dama, da suka hada da noma, sufuri, ilimi, kiwon lafiya da sauran bangarorin ci gaban tattalin arziki.
"Duk da ya ke waɗannan tsare-tsaren za su ɗauki lokaci, ina roƙonku da ku kara haƙuri yayin da muke ɗaukar matakan rage tasirin tsadar rayuwar da ake fuskanta."

Kara karanta wannan

Najeriya @64: An gano illolin talauci, kungiya ta kawowa Tinubu shawara

- A cewar gwamnan.

Gwamnan Filato zai magance rashin tsaro

Gwamnan ya kuma bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da dora yakininsu kan gwamnatinsa yana mai cewa gwamnati ta dukufa kan maido da tsaro da zaman lafiya a jihar.

“Hukumomin tsaronmu suna aiki tukuru, kuma ana samun ci gaba a yaki da rashin tsaro. Za mu ci gaba da ba da fifiko ga lafiyarku da kuma jin daɗinku."

- A cewar gwamnan.

Gwamna Muftwang ya ce bai kamata ‘yan Nijeriya su manta da cewa duk da kalubalen da ake fuskanta, kasar na ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya ba.

Najeriya @64: Sakonni 7 daga jawabin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya isar da muhimman sakonni bakwai a jawabin da ya gabatar na ranar murnar samun 'yancin Najeriya.

Mahimman batutuwa daga jawabinsa sun haɗa da sauye-sauyen tattalin arziki, ci gaban tsaro, da kuma shirye-shiryen ƙarfafa matasa kamar yadda muka ruwaito.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.