Gwamnan Bauchi Ya Yafewa Fursunoni 153, Ya Basu N50,000 Kudin Jari

Gwamnan Bauchi Ya Yafewa Fursunoni 153, Ya Basu N50,000 Kudin Jari

  • Gwamnatin jihar Bauchi ta yafewa fursunoni 153 da suka kananan laifuka da aka jefa gidajen yari
  • Yace cigaba da tsaresu a gidajen yari bisa kananan laifi suna cakuduwa da manyan yan ta'adda baida amfani
  • Yace wadanda aka saki tuni sun koyi sana'o'i daban-daban kuma sun hada masa takalmi

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta yafewa fursunoni 153 da suka kananan laifuka da aka jefa gdajen yari daban-daban a fadin jihar ta Arewa maso gabas.

Gwamnan jihar, Bala Mohammed Abdulkadir, ya bayyana hakan a bikin yafewa fursunonin da akayi ranar Juma'a.

Gwamnan yace za'a baiwa kowani fursuna kudi N50,000 domin su ja jari yayinda suke shirin komawa gida.

A cewarsa, cigaba da tsaresu a gidajen yari bisa kananan laifi suna cakuduwa da manyan yan ta'adda ba abu amfani bane.

Kara karanta wannan

"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Dan Jarida Makaho Yayi Tsokaci Kan Aure da rayuwarsa

Yace:

"Zamu baiwa kowani Fursuna da aka saki N50,000 don ya fara wani kasuwanci nasa da niyyar dogaro da kai."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun yi imanin cewa taimakawa talaka da kudi na hanya mafi kyau wajen tabbatar da zaman lafiya, da tsaro.
"Babu bukatar ajiye wadannan mutane tare da manyan masu laifi a (gidan yari)."
"Zan yafe musu kuma ina kyautata zaton cew zasu koma gidajensu su zama mutanen kirki ga iyalansu, jiharmu da kasa baki daya."
Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Gwamnan Bauchi Ya Yafewa Fursunoni 153, Ya Basu N50,000 Kudin Jari Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Gwamnan ya kwadaitar da Fursunonin su kasance mafi yiwa dokar kasa 'da'a kuma suyi amfani da kudin da aka basu wajen abu mai amfani ga kawunansu.

A taron, Babbar Alkalin jihar, Rabi Umar, ta ce yafewa fursunoni na daga cikin hurumin gwamnan.

Tace wannan mataki zai rage cinkoso a gidajen gyara hali a jihar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yau Zan Kara Adadin Hadimaina Zuwa 100,000: Gwamna Nyesom Wike

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel