Najeriya @64: Muhimman Abubuwa 7 daga Jawabin Tinubu na Ranar Samun 'Yanci
- Jawabin shugaban kasa Bola Tinubu na ranar samun ‘yancin kai a 2024 ya nuna tsayin daka da ci gaban da al’ummar kasar ke samu
- Muhimman batutuwa daga jawabinsa sun haɗa da sauye-sauyen tattalin arziki, ci gaban tsaro, da kuma shirye-shiryen ƙarfafa matasa
- Jawabin Tinubu na ranar 'yanci ya nuna aniyar hadin kan kasa da kuma kyakkyawar makoma ga daukacin ‘yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Yayin da Najeriya ke cika shekaru 64 da samun 'yancin kai, al'ummar kasar sun cika da murna da kuma jinjinawa 'yan mazan jiya da suka tabbatar da 'yancin.
Fadi tashin da aka yi daga ranar 1 ga Oktoba, 1960 zuwa yau, na cike da nasarori da kuma kalubale. Sai dai kuma, gumin magabatanmu bai zuba kasa a banza ba.
Jawabin murnar 'yancin kan Najeriya
Jawabin ranar samun ‘yancin kai na bana da Bola Tinubu ya yi, ya nuna harsashin da aka sanya domin ci gaban kasar a gaba, kamar yadda Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin nasa ya tabo batutuwa masu muhimmanci kamar sauye-sauyen tattalin arziki, tsaro, bunkasa aikin gona, sauye sauyen makamashi, karfafa matasa, da hadin kan kasa.
Ga muhimman abubuwa guda bakwai daga jawabin ranar samun ‘yancin kai na shugaba Tinubu a 2024:
1. Waiwaye kan shekarun 'yanci
Shugaba Bola Tinubu ya fara jawabinsa ne da yin tsokaci kan fadi tashin Najeriya a shekaru 64 da kasar ta yi tun bayan samun ‘yancin kai.
Duk da tarin kalubale, ya ce kasar ba ta nuna gazawa ba sakamakon hadin kan 'yan kasar, inda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai karfi da cikakken iko.
2. Gyaran tattalin arziki
Shugaba Tinubu ya bayyana gagarumin garambawul na tattalin arziki da gwamnatin tarayyar ta ke yi da nufin rage radadin wahala da inganta rayuwa.
Musamman ma, ya ce gwamnatinsa ta jawo hannun jarin sama da dala biliyan 30 daga kasashen waje a cikin shekarar da ta gabata.
Kazalika, gwamnatinsa ta biya dala biliyan bakwai da kuma sama da Naira tiriliyan 30 na wasu basussukan cikin gida da waje.
3. Samar da tsaro da yakar ta'addanci
Shugaban ya nuna alfahari da cewa an samu ci gaba a yaki da ta'addanci da 'yan fashin daji a Najeriya.
Sama da kwamandojin ‘yan Boko Haram 300 ne aka kashe, lamarin da ya maido da zaman lafiya a daruruwan garuruwan Arewa tare da ba dubban mutane damar komawa gida.
4. Cigaban harkar noma
Gwamnatin Tinubu na samun cigaba a harkar noma ta hanyar saka hannun jari a harkar noma na zamani.
Manoma na karbar taki da taraktoci, kuma an shirya kafa wata cibiyar hada taraktocin John Deere 2,000 da sauran kayan aikin gona.
5. Sauye sauyen makamashi
Kokarin shugaban kasa a kan iskar gas din CNG domin ganin ya isa lungu da sakon kasar nan ya na ci gaba da tabbata.
Gwamnatin Tarayya tana kuma taimaka wa jihohi wajen samun motocin CNG domin sufurin jama'a cikin farashi mai rahusa.
6. Tallafawa matasa
Wani babban abin jan hankali a jawabin shi ne sanarwar taron matasa na kasa na kwanaki 30 domin magance kalubale da damarmakin da matasan Najeriya ke fuskanta.
An samar da shirin 3MTT domin samar da kwararrun matasa kan fasa a kasar, yayin da asusun ba da lamunin karatu (NELFUND) ke ba da rancen kudi ga ɗalibai.
7. Hadin kan kasa da zaman lafiya
Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da hadin kan kasa da dorewar kyakkyawar zamantakewa.
Ya kuma jaddada mahimmancin kasuwanci da saukin gudanar da shi, tare da karfafa gwiwar ‘yan Najeriya da su jajirce a kan ci gaban kasar domin samun kyakkyawar makoma.
Jagororin neman 'yancin kai a Najeriya
Tun da fari, mun ruwaito cewa daga Abubakar Tafawa Balewa zuwa Nnamdi Azikiwe, mutane da dama sun sadaukar da rayukansu domin 'yancin Najeriya.
A yayin da Najeriya ke murnar cika shekaru 64 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, Legit Hausa ta tattaro bayanin jagorori 10 da suka nemawar kasar 'yanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng