Najeriya @64: Tinubu Ya Kira Gwamnonin Jihohi 5 a Arewa, Ya Yaba Masu a Jawabinsa

Najeriya @64: Tinubu Ya Kira Gwamnonin Jihohi 5 a Arewa, Ya Yaba Masu a Jawabinsa

  • Shugaba Bola Tinubu ya ba yan Najeriya tabbacin yana daukar matakai masu muhimmanci domin rage tsadar rayuwa
  • Mai girma Tinubu ya yabawa wasu gwamnonin Arewacin Najeriya kan kokarin da suka yi wurin rungumar harkokin noma
  • Shugaban ya kuma roki sauran gwamnonin jihohin Najeriya da su ba da karfi da kuma hadin kai ga Gwamnatin Tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi jawabi ga yan kasa inda ya roke su kan cigaba da nuna juriya.

Tinubu ya yabawa wasu jihohin Arewacin Najeriya da kuma na bangaren Kudu maso Yamma kan harkokin noma.

Tinubu ya yabawa wasu gwamnonin Arewacin Najeriya
Bola Tinubu ya ba yan Najeriya tabbacin kawo karshen tsadar rayuwa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya sake ba yan Najeriya tabbaci

Kara karanta wannan

Ranar yanci: Yadda aka kashe jagororin yan ta'adda 300 a Najeriya

Shugaban ya fadi haka ne yayin jawabinsa na cika shekaru 64 na yancin kai da hadiminsa, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ba da tabbaci ga yan Najeriya kan irin matakan da ya ke dauka domin rage radadin halin kunci a kasar.

Ya yabawa gwamnonin jihohin Kebbi da Kwara da Jigawa da Nasarawa da kuma Niger kan bunkasa harkokin noma.

Har ila yau, ya yabi sauran gwamnonin yankin da ya fito na Kudu maso Yamma kan yadda suka rungumi harkar noma.

Tinubu ya yabawa wasu gwamnonin jihohin Arewa

"Yan uwana yan Najeriya, ina mai ba ku tabbacin muna daukar matakai da za su rage tsadar rayuwa da ake ciki."
"Ina yabawa gwamnonin Kebbi da Niger da Kwara da Nasarawa da Jigawa da kuma gwamnonin Kudu maso Yamma kan rungumar harkokin noma da bunkasa shi."

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Abin da Tinubu ya fada game da halin kunci, ya roki yan kasa

"Ina mai kira da sauran gwamnonin Najeriya da su marawa Gwamnatin Tarayya baya wurin inganta noma zuwa na zamani."

- Bola Tinubu

Tinubu ya ce gwamnatinsa tana ba da gudunmawa wurin samar da takin zamani da motoci da sauran kayan bunkasa harkokin noma.

Jawabin Tinubu game da halin kunci

Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi jawabi mai kama hankali ga yan kasar kan halin kunci da ake ciki.

Tinubu ya ce tabbas ana cikin wani hali kuma za a iya fuskantar kalubale a gaba amma komai zai dawo daidai nan gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.