Ranar Yanci: Yadda Aka Kashe Jagororin Yan Ta’adda 300 a Najeriya
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi jawabi ga yan kasa kan murnar cika shekaru 64 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka
- Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarar hallaka daruruwan mayan yan ta'adda a shekara daya
- A karkashin haka, shugaban kasar ya ce yana cike da farin ciki kan gagarumar nasarar da sojojin Najeriya ke cigaba da samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna farin ciki kan yadda ake cigaba da samun nasara kan yan ta'adda.
Bola Tinubu ya bayyana farin cikin ne yayin da yake bayani ga yan kasa kan murnar cika shekaru 64 da samun yancin kai.
Legit ta tattaro bayanan da shugaban kasar ya yi ne a cikin wani sako da shafin Aso Rock Villa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe jagororin yan ta'adda 300
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa jami'an tsaron Najeriya sun samu gagarumar nasara kan yan ta'adda a cikin shekara daya.
Bola Tinubu ya ce an kashe jagororin yan ta'adda tsakanin Boko Haram da yan bindiga sama da 300 a Najeriya.
Burin Tinubu kan tsaron Najeriya
Shugaban kasar ya ce babban burinsa shi ne kawar da yan bindiga, masu garkuwa da mutane da Boko Haram.
Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da ƙoƙari wajen samar da zaman lafiya da kawo karshen yan ta'adda.
Tinubu ya nuna farin ciki a kan tsaro
Bola Ahmed Tinubu ya ce a yanzu haka sun dawo da zaman lafiya a garuruwa da dama kuma dubban mutane sun koma gidajensu.
Saboda haka ya ce yana mai matukar farin ciki kan yadda jami'an tsaro ke cigaba da samun nasara kan miyagu a Najeriya.
An fara zanga zangar Oktoba a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa daruruwan matasan Najeriya sun fito kan tituna domin fara zanga zangar Oktoba a birnin tarayya Abuja.
Matasan sun fito kan tituna ne dauke da alluna suna kokawa kan yadda aka shiga yanayin wahalar rayuwa a Najeriya a mulkin Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng