Oktoba: Zanga Zanga Ta Barke Ana Tsaka da Bikin Ranar Yanci

Oktoba: Zanga Zanga Ta Barke Ana Tsaka da Bikin Ranar Yanci

  • Matasan Najeriya sun fito kan tituna domin fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da suka shirya a farkon watan Oktoba
  • Tarin matasa ne suka fito suna daga alluna suna cewa suna jin yunwa kuma suna kira a kan gwamnatin Bola Tinubu ta dauki mataki
  • A yau Talata, 1 ga Oktoba Najeriya ke murnar cika shekaru 64 da samun yanci daga turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Matasan Najeriya sun fito kan tituna domin fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

A birnin tarayya Abuja, matasan sun fito dauke da alluna da suke kira ga gwamnatin tarayya kan kawar da zalunci a tsarin shugabanci.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya damu da matasa, ya shirya yin taron kasa na kwanaki 30

Zanga zanga
An fara zanga zangar Oktoba a Najeriya. Hoto: Omoyele Sowore
Asali: Getty Images

Legit ta gano yadda zanga zangar ke gudana ne a cikin wani bidiyo da tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatun masu zanga zangar Oktoba

Legit ta ruwaito cewa masu zanga zangar tsadar rayuwa sun gabatar da bukatu 17 ga gwamnatin tarayya.

Matasan sun bayyana cewa idan ba a biya musu bukatunsu ba za su cigaba da yin zanga-zanga a fadin ƙasar nan.

An fara zanga zanga a birnin Abuja

Matasan Najeriya sun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu a birnin tarayya Abuja.

A cikin wani bidiyo, matasan suna yawo ka kan titi ne suna cewa yunwa suke ji saboda haka a dauki mataki.

Bukatun masu zanga zangar Oktoba

Daga cikin abin da masu zanga zangar ke cewa kawai buƙatar inganta Ilimi da kawo saukin rayuwa.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta gargaɗi mutanen Kano kan zanga zangar da ake shirin yi

Wani matashi ya koka kan cewa rayuwa ta yi tsada inda ake sayen litar man fetur a sama da N1,000 a Najeriya.

Sun bayyana cewa ba yadda za a yi su yi shiru bayan an jefa su cikin wahalar rayuwa da gangan a kasar nan.

Zanga zanga: Yan sanda sun yi shiri

A wani rahoton, kun ji cewa matasan Najeriya sun ce ba makawa kan fitowa zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Oktoban 2024.

Rundunar yan sandan Najeriya ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro da ganin cewa bata gari ba su kwace ragamar zanga zangar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng