Najeriya @64: An Gano Illolin Talauci, Kungiya Ta Kawowa Tinubu Shawara

Najeriya @64: An Gano Illolin Talauci, Kungiya Ta Kawowa Tinubu Shawara

  • A yau ne Najeriya ta cika shekaru 64 da samun yancin kai, inda tuni aka fara ba gwamnati shawari kan cigaban kasa
  • Kungiyar Association of Seadogs, Pyrates Confraternity ta ce akwai matsalolin yunwa da rashin tsaro a kasar nan
  • Saboda haka ta shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan matakan da za su kawo cigaba da kwanciyar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - A daidai lokacin da kasar nan ke bikin zagayowar cikar nan shekararta 64 da samun yancin kai, kungiyar Association of Seadogs, Pyrates Confraternity ta gano matsalar kasar nan.

Kara karanta wannan

Zanga Zanga: Kungiyoyin Arewa sun amsa kiran fitowa tituna a ranar 1 ga Oktoba

Kungiyar da Wole Soyinka da wasu dalibai shida su ka kafa a shekarar 1952 a fafutukar jawo hankali wajen inganta rayuwar al'uma.

Tinubu
An shawarci Tinubu kan matsalolin kasa Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa kungiyar, karkashin jagorancin Dr Joseph Oteri ta ce za a cigaba da samun rashin tsaro idan gwamnati ba ta gyara matsalolin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu matsaloli su ka addabi Najeriya?

Arise TV ta tattaro cewa kungiyar NAS ta ce akwai talauci,wanda ya jawo yunwa da karuwar ayyukan rashin tsaro a fadin kasa.

Sauran matsalolin da kungiyar ta bayyana cewa su na addabar kasar nan sun hada da yawaitar yara marasa zuwa makaranta, rashin tsaro da lalatattun hanyoyi.

Kungiya ta ba Bola Tinubu shawara kan Najeriya

Kungiyar NAS ta gargadi gwamnatin tarayya kan kama jama'ar da su ke fitowa zanga-zanga domin nuna kin amincewa da wasu daga cikin manufofinta.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya kare manufofin gwamnati, ya jaddada alfanun cire tallafin fetur

Dr Joseph Oteri ya ce kamata ya yi gwamnatin ta yi hobbasa wajen magance matsalolin domin wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a kasa.

Gwamna ya nemi yi wa Najeriya addu'a

A baya mun wallafa cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya shawarci yan kasar nan da su dage da addu'a domin a cimma manufofin cigaba da zaman lafiya

Ya shawarci yan kasa su zama nagari, domin ta haka ne za a rage lalata kadarorin da gwamnati ta samar saboda yan kasa da samun kwanciyar hankali a sassan kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.