An Kama Dan Fashin da Ya Addabi Mutane, Ya Tona inda Ya Sayo Makamai
- Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Jigawa ta yi nasara kan wasu yan fashi da makami da suka addabi al'ummar Arewa
- Cikin miyagun da rundunar ta kama, har da babban ɗan fashi da makami da ya addabi mutane a Jigawa da wasu sassan Arewa
- Yan sanda sun tabbatar da cewa an kama babban dan fashin ne a jihar Benue bayan samun bayanan sirri a kan moɓoyarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta yi nasarar cafke ƙasurgumin dan fashi da makami da ya addabi al'ummar Arewa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dan fashin da ake zargin ya shahara da ayyukan ta'addanci a tsakanin kananan hukumomin Ringim da Dutse a Jigawa.
Kakakin yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam ya tabbatarwa Legit cewa an kama dan fashin da ake zargin da makamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama babban dan fashi a Arewa
Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta sanar da cafke wanda ake zargi da fashi da makami mai suna Buhari Ya'u.
Dan fashin da ake zargin ya shahara da sace sace kuma an cafke shi ne tun ranar 10 ga Satumba a jihar Benue bayan samun bayanan sirri a kansa.
Dan fashi da makami ya yi kisan kai
Ana zargin Buhari Ya'u da fashin da makami da ya jawo kisan wani mutum mai suna Murtala Ja'afar dan shekaru 40.
A bisa zargin, Buhari Ya'u ya jagoranci fashi da makami ne a yankin Kwanar Shafa a karamar hukumar Ringim kuma an samu bindiga yayin da aka kai samame gidansa.
Dan fashin ya amsa laifinsa
A yayin da ake yi masa tambayoyi, Buhari Ya'u ya tabbatar da cewa yana fashi da makami a hanyar Jahun zuwa Gujungu, Dindibis zuwa Gamoji da hanyar Shuwarin zuwa Kiyawa.
Buhari Ya'u ya ce yana fashi ne tare da wasu mutane hudu kuma ya saye makami ne a wajen wani mutum da aka fi sani da Alhaji Ja'o a ƙaramar hukuma Ajingi a Kano a kan N450,000.
An kama dan fashi a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta yi nasarar cafke wani gungun yan fashi da suka addabi mutane a karamar hukumar Misau.
Ana zargin cewa yan fashin sun shiga wani gida da bindiga suka kwace makudan kudi da kayayyaki masu muhimmanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng