N70,000: Jerin Gwamnonin Arewa da ke Shirin Fara Karin Albashin Ma'aikata
- Wasu gwamnonin Arewa sun yi alkawarin fara biyan mafi ƙarancin albashi zuwa N70,000 da zarar gwamnatin tarayya ta fara
- A makon da ya wuce gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na N70,000 a kowane wata
- A wannan rahoto, mun tatttaro muku jerin gwamnonin Arewa da suka yi alkawarin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Wasu gwamnonin Arewa sun dauki alkawarin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.
Gwamnonin sun yi alkawarin fara karin albashin ne da zarar gwamnatin tarayya ta yi wa ma'aikata kari.
A wannan rahoton, mun tatttaro muku jerin gwamnonin Arewa da suka yi alkawarin fara karin albashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin da suka yi alkawarin karin albashi
1. Gwamnan Nasarawa
Punch ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana cewa a shirye ta ke domin yiwa ma'aikata karin albashi.
A kwanakin baya ne hadimin gwamna Abdullahi Sule, Peter Ahemba ya ce gwamnan yana jiran gwamnatin tarayya ne ta fara karin albashi.
2. Gwamnan Sokoto
Gwamnan Sokoto ya bayyana cewa gwamnatinsa tana shirye domin fara biyan ma'aikata N70,000.
Ahmed Aliyu ya ce gwamnatinsa tana kan shirye shiryen karin albashin ma'aikata a jihar Sokoto zuwa N70,000.
3. Gwamnan Gombe
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa ba za ta yi wasa wajen karin albashi ba.
Legit ta ruwaito cewa gwamna Inuwa Yahaya ya ce yana jiran gwamnatin tarayya ne ta fara karin albashi ga ma'aikata.
Sauran gwamnoni da karin albashi
Gwamnonin jihohin Kebbi, Katsina, Taraba, Kogi da Kano duk sun yi alkawarin karin albashi ga ma'aikata.
Haka zalika gwamnan Zamfara ya ce zai fara biyan sabon albashi da zarar kwamiti sun kammala aikinsu.
Gwamnan Adamawa ya fara biyan sabon albashi yayin da kallo ya koma kan gwamnonin da suka yi alkawrin fara biyan N70,000 bayan gwamnatin tarayya.
Anambra: Gwamna zai yi karin albashi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Chukwuma Soludo ya sanar da cewa zai fara biyan ma'aikatan jiharsa ta Anambra sabon albashin N70,0000 a watan Oktoba.
Gwamnan Chukwuma Soludo ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da dukkanin shugabannin makarantun firamare da sakandare a Awka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng