Kaduna: Sojojin Saman Najeriya Sun Kashe Farar Hula 25 a Wani Harin Bam?

Kaduna: Sojojin Saman Najeriya Sun Kashe Farar Hula 25 a Wani Harin Bam?

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta warware rudanin da aka samu game da wani harin sama da ta kai dajin Yadi da ke jihar Kaduna
  • Mazauna kuayen Jika da Kolo sun yi ikirarin cewa sama da mutane 25 ne suka mutu a harin sama da rundunar sojin ta kai yankin
  • Sai dai rundunar sojin ta dage kan cewa babu gidajen fararen hula a yankin da ta kai harin kuma ta yi nasarar samun wadanda ta hara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta ikirarin kashe fararen hula a wani harin da ta kai ta sama a jihar Kaduna.

Rundunar ta dage cewa ta kaddamar da harin ne bayan samun sahihin bayanan sirri game da wani babban sansanin ‘yan ta’adda da ke dajin Yadi.

Kara karanta wannan

Kaduna: An zargi sojoji da sake jefa bama bamai a masallaci aka kashe bayin Allah

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi bayani kan harin da ta kai jihar Kaduna
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ba ta saki bama bamai kan fararen hula a jihar Kaduna ba. Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

"Dalilin kai hari a Kaduna" - Sojoji

Rundunar sojin saman ta bayyana cewa harin na baya-bayan nan da aka kai ta sama wani bangare ne na atisayen WHIRL PUNCH (OPWP) inji The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar atisayen WHIRL PUNCH (OPWP) shi ne kai hari a maboyar ‘yan ta’adda a Kaduna da kewaye inji rundunar sojin saman.

Jaridar This Day ta rahoto Kyaftin Kabiru Ali, mataimakin daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojin ya kara da cewa:

"Harin ya mayar da hankali ne kan wani sansani da fitattun jagororin ‘yan ta’adda ke amfani da shi, ciki har da Kadade Gurgu, na hannun daman Dogo Gide."

Sojoji sun karyata kashe fararen hula

Rundunar sojin ta ce nau'urarta ta ISR ta ga motsin 'yan ta'adda da ke guduwa bayan jiyo karar jirgin sama, lamarin da ya sa ta sakar masu bama bamai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza da miyagu, sun hallaka 'yan ta'adda da ceto mutane da dama

Sai dai rundunar ta ce ta samu abin harinta, kuma babu gidajen fararen hula a yankin yayin da ta dage kan cewa 'yan bindiga ne ta farmaka.

“Rahotanni daga majiyoyi, ciki har da masu ba mu bayanan sirri, sun tabbatar da cewa an lalata mabuyar 'yan ta'addan gaba daya, kuma an kashe ‘yan bindiga da dama.
"Babu wani masallaci a ko gidajen farar hula a wurin da aka kai harin, kuma an yi nasarar wargaza hanyar sadarwar ‘yan ta’addan."

- A cewar Kyaftin Kabiru.

An zargi sojoji da kashe farar hula

Tun da fari, mun ruwaito cewa mazauna karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna sun yi ikirarin cewa sojojin saman Najeriya sun jefa masu bama bamai.

Mazauna yankin Jika da Kolo sun ce harin bam din sojojin ya kashe mutanensu 25 da suka hada da masallata da 'yan kasuwa, a wani yanayi da ya yi kama da harin Tudun Biri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.