Rikici Ya Rincabe Tsakanin Dabar Yan Ta'adda 2, Rayuka Sun Salwanta

Rikici Ya Rincabe Tsakanin Dabar Yan Ta'adda 2, Rayuka Sun Salwanta

  • Yan bindiga daga bangarori biyu sun samu sabani inda aka yi mummunar arangamar da ta salwantar da ran fitinannen dan ta’adda
  • An kashe Kachalla Tsoho Lulu ne yayin da rikici ya kaure tsakanin bangarensa da na Kachalla Gajere, wanda yanzu ake nema ruwa a jallo
  • Haka kuma dakarun sojoji sun yi nasarar fatattakar yan ta'addan da ke karkashin Kachalla Gajere, bayan an ji masa munanan raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Wani dan bindiga, Kachalla Gajere ya kashe rikakken jagoran yan ta’adda, Kachalla Tsoho Lulu a wata arangama.

Lamarin ya afku a ranar 26 Satumba, 2024 a kusa da kauyen Kawaye a dajin Bagega da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe rikakken dan bindiga, Kachalla Mai Shayi a harin kwantan bauna

Ta'adda
Yan ta'adda sun kashe junansu a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Zagazola Makama, wani masanin tsaro a kasar nan ya wallafa cewa rikici ya barke tsakanin yan bindiga biyu, wanda dama an jima ana samun takun sako tsaninsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mabiya dan bindiga tsoho na neman kashe Gajere

Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa yanzu haka magoya bayan Kachalla Tsoho Lulu sun fara neman Kachalla Gajere ruwa a jallo domin daukar fansa.

Kachalla Tsoho Lulu gawurtaccen dan bindiga ne da ya addabi yankin Dan Kurmi da sauran karamar hukumar Maru a jihar a Zamfara.

Sauran wuraren da ya ke kai farmaki sun hada da Dan Ummaru zuwa Bena a karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi.

Yan bindiga sun yi arangama da sojoji

A wani lamarin na daban, dan bindiga Kachalla Gajere da aka fi sani da Mai Yar Gashi sun yi arangama da kauyen Dankurmi a kauyen Dansadau.

Kara karanta wannan

Kaduna: An zargi sojoji da sake jefa bama bamai a masallaci aka kashe bayin Allah

An kashe yan ta’adda da dama amma Kachalla Gajere ya tsere, sai dai ya samu raunuka sosai, kuma ana sa ran ba zai kai labari ba.

An kashe rikakken dan ta'adda

A baya kun ji wasu yan ta'adda sun samu kazamin rikicin ramuwar gayya, inda a nan ne yaran Kachalla Nagala su ka yi wa na hannun daman Kachalla Mai Bille kwanton bauna har su ka kashe shi.

A rikicin da yan ta'addan su ka rika kashe junansu, an halaka dan bindiga Kachalla Mai Shayi da wasu yaransa 12 a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.