'Kai Ka Jawo Tsadar Rayuwa': 'Dan Majalisa Ya Cire Tsoro Ya Fadawa Tinubu Gaskiya

'Kai Ka Jawo Tsadar Rayuwa': 'Dan Majalisa Ya Cire Tsoro Ya Fadawa Tinubu Gaskiya

  • Hon. Nnamdi Nzechi da ke wakiltar mazabar Ndokwa/Ukwani a majalisar wakilai ya ce shugaba Bola Tinubu ne ya jawo tsadar rayuwa
  • 'Dan majalisar ya ce gwamnatin Tinubu ta kawo tsare-tsaren da suka jefa 'yan kasar a mawuyacin hali ba tare da sassautawa ba
  • Nzechi ya kuma zargi shugaban kasar da kakabawa 'yan kasar harajin da ya kara jefa su a cikin matsin tattalin arziki da hawansa mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Delta - Wani dan majalisar wakilai, Nnamdi Nzechi ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kama Bola Tinubu da laifi kan wahalar da ake sha a kasar nan.

Hon. Nnamdi Nzechi ya yi wannan kiran ne a yammacin ranar Lahadi a garin Asaba, jihar Delta a wani taron kungiyar 'yan jarida ta NUJ.

Kara karanta wannan

'Ka yi hankali,' Dattawan Arewa sun gargadi Tinubu kan korar ministoci

Hon. Nnamdi Nzechi ya yi magana kan tsadar rayuwa a gwamnatin Tinubu
Dan majalisa ya ce Tinubu ne ya jefa 'yan Najeriya a tsadar rayuwa. Hoto: Hon Nnamdi Ezechi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

'Dan majalisa ya caccaki Tinubu

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa Hon. Nzechi na wakiltar mazabar Ndokwa/Ukwani da ke jihar Delta a majalisar wakilai ta tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisar ya koka kan cewa kasar ta koma baya kuma 'yan Najeriya na shan bakar azaba sakamakon manufofin tattalin arziki na gwamnatin Tinubu.

Hon. Nzechi wanda ya nuna muhimmancin kirkirar jihar Anioma a Kudu masu Kudu ya ce Tinubu ya ci gaba da aiwatar da tsare-tsarensa duk da illarsu ga al'ummar kasar.

Ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta kawo tsare-tsaren da suka gaza sauya rayuwar 'yan kasar saboda tarin haraji da aka sanyawa kananun 'yan kasuwa da kamfanoni.

"Tinubu ya jawo tsadar rayuwa" - Nzechi

A cewar Hon. Nzechi:

"Najeriya ba ta wani ci gaba karkashin gwamnatin APC. Tsare-tsaren da gwamnatin ke aiwatarwa sun gaza tasiri. An kakaba haraji mai yawa.

Kara karanta wannan

Cin hancin N15m: Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban EFCC da wasu mutum 2

"Tsare tsaren gwamnatin sun zamo tamkar garwashi ga jama'a wanda ya jawo tsadar rayuwa da kuma kunci ga 'yan kasar baki daya."

Dan majalisar ya kuma zargi Tinubu da gaza aiwatar da abubuwan da doka ta tanadar yana mai cewa sake fasalin kundin kasar ba shi ne matsala ba, aiwatar da dokar ne matsala.

APC ta zargi Tinubu kan tsadar rayuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC mai mulki ta amince da cewa tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu sun haifar da tsadar rayuwa.

Sakataren yada labaran APC, Barista Felix Morka ne ya bayyana hakan a martanin da ya mayarwa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar, Salihu Lukman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.