Bayan Tantancewar Sanatoci, Tinubu Ya Rantsar da Sabuwar Shugabar Alkalan Najeriya
- A ranar Litinin, 30 ga watan Satumbar 2024 ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da shugabar alkalan Najeriya ta 23
- An rahoto cewa Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalan a zauren majalisar zartarwar tarayya
- Kekere-Ekun ta sha alwashin zamantar da fannin shari'ar kasar inda ta ce za a rika gudanar da shari'o'in ta'addanci ta yanar gizo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalan Najeriya (CJN).
An gudanar da bikin rantsuwar ne a zauren majalisar zartarwar tarayya da ke Aso Rock Villa a ranar Litinin bayan da majalisar dattawa ta amince da nadin a makon jiya.
An ranstar da shugabar alkalai
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Kekere-Ekun ce shugabar alkalan Najeriya ta 23 kuma mace ta biyu da ta rike wannan mukami a tarihin kasar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, an ce an Kekere-Ekun ta kasance a ofishin a matsayin mukaddashiya bayan ritayar Olukayode Ariwoola a watan Agusta.
A yayin zaman tantance nadin da aka yi a zauren majalisar dattawa, shugabar alkalan ta amsa tambayoyi kan sauye-sauyen da take fatan aiwatarwa a bangaren shari’a.
"Zan tabbatar an zamanantar da fannin shari'a. Za mu kawo sauki wajen bibiyar shari'o'i da kuma tsawatar da alkalai idan suna wasa da ayyukansu."
- A cewar Kekere-Ekun.
Za a zamantar da fannin shari'a
Musamman a shari'o'in aikata laifuka, shugabar alkalan ta ta ce za a rika zaman shari'ar a yanar gizo idan har aka fahimci za a samu tsaiko a zaman kotun zahiri.
“Muna nazarin hanyoyin da za mu tabbatar da cewa ana yawan rage cunkoso a gidajen yari.
"Za a rika zaman shari'ar ta yanar gizo, rashin gabatar da wadanda ake tuhuma a gaban kotu shi ke kawo jinkirin shari'o'in aikata laifuffuka."
- A cewar shugabar alkalan.
Tinubu ya nada shugabar alkalai
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada sabuwar shugabar alkalan Najeriya (CJN) Kudirat Kekere-Ekun a fadar gwamnati da ke Aso Rock.
Tinubu ya amince da nadin Kekere-Ekun bayan ritayar Olukayode Ariwoola a watan Agusta da kuma shawarar majalisar shari'a ta kasa (NJC).
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng