Sojoji Sun Gwabza da Miyagu, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda da Ceto Mutane da Dama
- Rundunar sojin Najeriya ta gwabza kazamin fada da yan ta'adda a jihohi daban daban kuma ta samu nasarar hallaka su
- Bayan gwabza fadan, sojojin Najeriya sun ceto mutanen da yan bindigar suka kama cikin jeji, kimanin mutum 40 sun kubuta
- Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar sojin ta gwabza da yan ta'addar ne a jihohin Borno, Kaduna da wasu jihohin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Rundunar sojin Najeriya ta gwabza kazamar fada da yan bindiga da sauran yan ta'adda a jihohin Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun samu nasara kan miyagun yayin da suka hallaka wasu daga cikinsu.
Jaridar Punch ta wallafa cewa rundunar sojin ta kwato makamai da dama bayan kashe yan ta'addar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun gwabza da yan ta'adda a jihohi
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa sojojin Najeriya sun yi zazzafan bincike a hanyar Lafiya zuwa Keffi inda ta kama wani da ake zargi da safarar makamai.
Haka zalika a jihar Kaduna sojoji sun fafata da yan ta'adda kamar yadda rundunar ta fatattaki miyagu a jihohin Borno da Yobe.
Dakarun Sojoji sun kwato makamai a wurare
A jihar Yobe, sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe dan ta'adda daya da kwato bindiga ƙirar AK-47 da babur.
A jihar Borno ma yan ta'addar sun tsere sun bar tulin makamai bayan sun yi musayar wuta da sojojin Najeriya.
A jihar Kaduna, sojojin sun kashe yan ta'adda da dama tare da kwato tarin makamai da suke amfani da su.
Sojoji sun ceto mutane da dama
A yayin da aka fafata tsakanin sojojin Najeriya da yan ta'adda a karamar hukumar Kukawa a jihar Borno, yan ta'adda sun gudu sun bar mutane 38 da suka sace.
Shugaban rundunar sojin Najeriya ya yaba da ƙoƙarin sojojin inda ya ce rundunar za ta cigaba da yaki da yan ta'adda a Najeriya.
Sojoji sun yi nasara kan Boko Haram
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a Borno.
An ruwaito cewa sojojin sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin kai hari da ƴan ta'addan suka yi a kan titin hanyar Magumeri-Maiduguri a jihar.`
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng