Zanga Zangar Oktoba: Yan Sanda Sun yi Zazzafan Shiri a Jihohin Arewa da Kudu
- Matasan Najeriya sun ce ba makawa kan fitowa zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2024
- Rundunar yan sandan Najeriya ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro da ganin cewa bata gari ba su kwace ragamar zanga zangar ba
- A wasu jihohin, yan sanda sun zauna da shugabannin dalibai, yan kwadago da sauran masu ruwa da tsaki kan fitowa zanga zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Rundunar yan sandan Najeriya ta yi shiri na musamman kan tunkarar zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu.
Matasan Najeriya sun shirya fitowa zanga zangar ne a ranar 1 ga watan Oktoba a dukkan jihohin Najeriya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa yan sanda sun tattauna da kungiyoyin da suke shirin fita zanga zangar domin samar da mafita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Arewa: Shirin yan sanda kan zanga zanga
Rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce ta shirya tura jami'ai wuraren da ake tunanin za a taru domin yin zanga zangar, haka zalika a jihohin Neja da Kwara.
Kakakin yan sanda a jihar Neja, Wasiu Abiodum ya ce jami'an tsaro na shirye domin ganin ba a samu yan daba sun tayar da tarzoma ba.
Yan sanda a Kaduna, Borno, Kogi, Nasarawa da Katsina sun ce suna shirye domin dakile duk wani shirin bata gari ta tayar da fitina da kawo rikici.
Shirin yan sanda a Kudu kan zanga zanga
A Kudancin Najeriya ma rundunar yan sanda ta ce tana kan shirin ko-ta-kwana domin maganin duk wanda zai tayar da fitina.
Vanguard ta wallafa cewa kwamishinan yan sanda a jihar Ogun ya ce zai tura jami'ai wurare daban daban tun a ranar Litinin.
A jihohin Edo, Cross River da Bayelsa yan sanda sun ce ba za su bari a yi barna da sunan zanga zanga ba, kuma za su yi maganin duk wasu bata gari.
An sanar da lokutan zanga zanga a jihohi
A wani rahoton, kun ji cewa a ranar 1 ga Oktoba matasan Najeriya suka ce za su fito zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu a mulkin Bola Tinubu.
Yayin da ake saura kwana ɗaya da fara zanga zangar, matasa a kasar nan sun sanar da wurare da lokutan da za su fito a garuruwan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng