"Babu Wannan Zancen:" An Samu Bayani kan Shari'ar Zargin Matawalle da Ta'addanci

"Babu Wannan Zancen:" An Samu Bayani kan Shari'ar Zargin Matawalle da Ta'addanci

  • Masu kishin Zamfara sun musanta labarin cewa ana shari'a da tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle kan ta'addanci
  • An samu bullar labarin cewa wani mai fafutuka, Abubakar Dahiru ya shigar da kara kotu ya na neman a sahale tuhumar Matawalle
  • Shugaban kungiyar masu kishin Zamfara ya ce ana son batawa gwamnatin Matawalle suna domin ba shi da hannu cikin ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Kungiyar masu kishin jihar Zamfara sun karyata labarin fara zaman kotu kan zargin tsohon gwamnan jihar, Dr. Bello Matawalle da alaka da ta'addanci.

An samu bullar rahotanni da ke nuna cewa babbar kotun tarayya ta amince da rokon wani mai fafutuka, Abubakar Dahiru na a fara binciken karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu, gwamnoni sun yi ta'aziyyar uwar gidan gwamnan Akwa Ibom

Matawalle
Masu kishin Zamfara sun musanta shari'ar ta'addanci da Matawalle a Kotu Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ana ta samun zarge-zarge da ke alakanta Dr. Bello Matawalle da goyon bayan yan ta'adda da ta'addanci a jiharsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta'addanci: An musanta shari'ar Matawalle

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa shugaban kungiyar masu kishin Zamfara, Yusuf Sani da Sakatare Dahiru Nasiru, sun ce karya ake yadawa kan shari'a da Dr. Matawalle.

Sun kare tsohon gwamnan da cewa ko a baya, sai da ya yi fafutukar dakile ta'addanci a Zamfara inda ya kashe biliyoyin Naira domin cimma manufarsa.

"Matawalle zai iya kare kansa:" Kungiya

Masu kishin Zamfara sun yi ikirarin cewa ko da an kai karamin Minista, Bello Matawalle, zai iya kare kansa daga duk wani zargin ta'addanci da ake kokarin kakaba masa.

Kungiyar ta zargi gwamna Dauda Lawal Dare da kokarin cin mutuncin tsohuwar gwamnati tare da kalubalantar gwamnatin ta bayar da hujjojin zargin da ta ke yi wa Matawalle.

Kara karanta wannan

An damke jami'in tsaron da ke taimakon yan ta'adda a Zamfara

Yan bindiga sun farmaki kauyen Bello Matawalle

A baya kun ji cewa wasu yan bindiga sun kai farmaki kauyen karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle na Janboka da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Lamarin na zuwa ne yayin da aka jibge jami'an tsaro a Arewa maso Yammacin kasar nan, inda a wannan jikon aka sace mutane akalla 40 a ranar Asabar 28 Satumba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.