Oktoba: Masu Zanga Zanga Sun Saka Lokutan Farawa a Jihohi, APC Ta yi Gargadi

Oktoba: Masu Zanga Zanga Sun Saka Lokutan Farawa a Jihohi, APC Ta yi Gargadi

  • A ranar 1 ga Oktoba matasan Najeriya suka ce za su fito zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu a mulkin Bola Tinubu
  • Yayin da ake saura kwana ɗaya da fara zanga zangar, matasa sun sanar da wurare da lokutan da za su fito a garuruwan Najeriya
  • Jam'iyyun PDP da LP sun yi rubdugu ga APC kan maganar cewa bai kamata matasa su fito zanga zangar ba a wannan lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa sun kara shirin fitowa kan titunan Najeriya domin nuna fushinsu kan gwamnati.

An samu sabani tsakanin jam'iyyun siyasa a Najeriya a kan fitowa zanga zangar a ranar yancin kasa.

Kara karanta wannan

Shirin zanga zangar 1 ga Oktoba ya kankama, an aika sako ga 'yan sanda

Zanga zanga
Matasa sun saka lokutan fita zanga zanga a Najeriya. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Facebook

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya wallafa wasu wuraren da za su taru domin fara zanga zangar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu wurare da lokutan zanga zanga

Punch ta ruwaito cewa masu zanga zangar sun ce za su taru a dandalin Eagle Square a birnin tarayya Abuja. A Legas kuma za su taru a karkashin gada a Ikeja.

A jihar Oyo, matasan sun ce za su fito zanga zangar ne da misalin karfe 8:00 na safe a shatale-talen Mokola da ke Ibadan.

Omoyele Sowore ya bayyana cewa suna shirye tsaf domin fara zanga zangar da misalin karfe 7:00 na safe a Abuja sai kuma Legas za su fito karfe 7:30 na safe.

APC ta yi gargadi kan zanga zanga

Daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim ya ce kada matasa su rudu da yan adawa wajen fitowa zanga zanga a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zanga zangar Oktoba: Matasan Arewa sun fadi matsayarsu kan hawa tituna

Sai dai daraktan yada labaran PDP, Abdullahi Ibrahim ya ce APC ke azabtar da mutane a Najeriya saboda haka ne matasa suka fito zanga zangar.

Haka zalika daraktan yada labaran LP, Obiora Ifoh ya ce ba wanda zai zargi jam'iyyun adawa da shirya zanga zangar saboda APC ce ta jefa mutane a damuwa.

Kungiyar Arewa ta fita daga zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar matasa a Arewa ta janye daga shiga zanga-zangar da ake shirin yi a ranar Talata 1 ga watan Oktoban 2024.

Kungiyar Arewa Youths for Peaceful Coexistence ta shawarci masu shirin yin zanga-zangar da su nemo hanyar tattaunawa da gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng