'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban NURTW da Wasu Mutum 3 a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban NURTW da Wasu Mutum 3 a Kaduna

  • Wasu ƴan bindiga sun sake sace shugaban ƙungiyar NURTW a ƙauyen Kidandan da ke ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan sun sace shugaban ne tare da wasu yara ƙanana guda uku bayan sun kai farmaki a ƙauyen cikin dare
  • A lokacin baya da aka sace shugaban na NURTW sai da ya kwashe kwanaki 60 a hannun ƴan binɗigan kafin ya samu ƴanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ƙungiyar ma’aikatan sufuri ta ƙasa (NURTW) a ƙauyen Kidandan da ke ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kuma sace ƴaƴan wani ma’aikacin lafiya a ƙauyen guda uku bayan sun kai farmaki da misalin ƙarfe 9:30 na daren ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon APC ya kare Tinubu, ya ba 'yan Najeriya shawara

'Yan bindiga sun sace shugaban NURTW a Kaduna
'Yan bindiga sun sace mutum hudu a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ce ƴan bindigan ba su daɗe da sako shugaban ƙungiyar ta NURTW mai suna Tasiu Habibu, bayan ya kwashe kusan kwanaki 60 a hannunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuɓuta daga hannun ƴan bindigan ne bayan an biya kuɗin fansa, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Yadda ƴan bindiga suka sace mutanen

Wani mazaunin garin, Sanusi Kidandan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce yawancin mutanen ƙauyen ba su iya barci ba saboda harbin bindiga.

"Mahaifin yaran uku makwabcin shugaban NURTW ne. Amma sun ɗauki yaran ne kawai, dukkansu ƙanana. Gaba ɗaya mutum huɗu suka ɗauka."
"Ƴan bindigan sun yi ta harbe-harbe a lokacin da suka kai farmakin. Sun zo ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare."

- Sanusi Kidandan

A cewarsa, an garzaya da wani ɗan ƙauyen mai suna Idris Jibril zuwa asibiti bayan ƴan bindigan sun harbe shi.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma rundunar ƴan sanda.

Ba a samu jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan.

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun sace wasu manoma shida suna tsaka da ke aiki a gona a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun sace manoman ne da suka haɗa da maza huɗu da mata biyu a ƙauyen Gidan Busa da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng