Bello Turji: Sanatan APC Ya Soki Matawalle da Sojoji, Ya Yabawa Kokarin Jonathan

Bello Turji: Sanatan APC Ya Soki Matawalle da Sojoji, Ya Yabawa Kokarin Jonathan

  • Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya koka kan yadda ta'addanci ke kara kamari tare da gagara kawo karshensu
  • Ndume ya bayyana cewa a karshen mulkin Goodluck Jonathan ya yi nasarar fatattakar yan Boko Haram
  • Ndume ya nuna damuwa game da yadda hafsoshin tsaro suka gagara kawo karshen dan ta'adda, Bello Turji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume ya koka kan yadda hafsoshin tsaro suka gagara kama rikakken dan ta'adda, Bello Turji.

Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya dakile Boko Haram a karshen mulkinsa.

Sanatan APC, Ndume ya koka kan karuwar ta'addanci da Bello Turji
Sanata Ali Ndume ya nuna damuwa kan gagara dakile ta'addanci a Najeriya. Hoto: Senator Ali Ndume.
Asali: UGC

Ta'addanci: Ndume ya caccaki hafsoshin tsaro

Kara karanta wannan

Sanata ya cigaba da tonon silili, ya fallasa rashin gaskiyar ‘yan siyasar kasar nan

Ndume ya fadi haka ne yayin hira da yan jaridu a bayan taron Majalisar Tarayya kan duba kundin tsarin mulki a Kano, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya ce Jonathan ya yi nasarar fatattakar yan Boko Haram daga wurare da dama a karshen mulkinsa a shekarar 2014.

Ya tuno yadda jami'an sojojin haya daga kasar Afirka ta Kudu da hadin guiwar sojojin Najeriya suka yi nasarar fatattakarsu.

Ndume ya soki sojoji kan Bello Turji

"Na kasance shugaban kwamitin sojoji kuma daga jihar Borno, manyan kalubale da na ke fuskanta sune Boko Haram da masu garkuwa da IPOB."
"Dukan wadannan idan gwamnati da gaske ta ke yi a cikin watanni shida za ta gama da su ko karkari shekara daya."
"Yan ta'addan suna can suna daukar bidiyo tare da yadawa a kafofin sadarwa, amma hafsoshin tsaro da Minista a Sokoto sun gagara kamo Turji."

Kara karanta wannan

Yemi Cardoso ya yi rugu rugu da darajar Naira cikin watanni 12 a Bankin CBN

- Sanata Ali Ndume

Ndume ya yi tone-tone kan yan siyasa

Kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya na ganin an tara barayi da marasa gaskiya a cikin masu rike da mukamai a yau.

Sanatan na Kudancin jihar Borno ya ce mafi yawan ‘yan siyasa da wadanda ke kujerun gwamnati barayi ne ba su da gaskiya.

Wadanda suka kubuta daga wannan danyen aiki in ji Ndume su ne wasu kalilan da Ndume ya ce su na da tsoron Ubangiji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.