Shirin Zanga Zangar 1 ga Oktoba Ya Kankama, An Aika Sako ga 'Yan Sanda
- Wadanda suka shirya zanga-zangar 1 ga watan Oktobar 2024 sun bukaci rundunar 'yan sanda ta basu tsaro a yayin da suke zanga zangar
- Masu shirya zanga zangar sun kuma sanar da 'yan sandan cewa gangamin zai gudana ne a filin Eagle Square na Abuja da gadar Ikeja, a Legas
- Wasu da Legit Hausa ta zanta da su sun nuna damuwa kan yiwuwar zanga zangar 1 ga Oktoba ta koma tashin hankali kamar ta Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wadanda suka shirya zanga-zangar #FearlessOctober1 sun bayyana cewa 'yan sanda, DSS da sojoji ba za su hana su gudanar da zanga-zangar ba kamar yadda suka tsara.
Masu shirya gangamin sun kuma rubutawa Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun takardar neman tsaro a lokacin zanga-zangar da za su fara 1 ga watan Oktobar 2024.
Shirin zanga-zangar 1 ga Oktoba
Wadanda suka shirya zanga-zangar sun lura cewa zanga-zangar wani hakki ne na 'yan kasa kuma ba za su mika wuya ga barazanar kowa ba, inji rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Talata 1 ga Oktoba ne Najeriya za ta yi bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai, ranar da wasu matasa suka shirya gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa.
Kodinetan zanga zangar 'Take It Back' na kasa, Juwon Sanyaolu, da daraktan hado kan jama'a na kungiyar, Damilare Adenola, sun ce tuni aka kammala shiryawa wannan gangamin.
An bayyana wuraren zanga zanga
Sun kara da cewa ‘yan Najeriya za su fito kwansu da kwarkwatarsu daga sassa daban-daban na kasar domin gudanar da zanga-zangar.
“Mun aikawa Sufeto Janar na ‘yan sanda takarda, mun sanar da shi wuraren da za mu gudanar da zanga-zangar tare da tunatar da shi hakkin masu zanga zangar na samun tsaro."
- A cewar Sanyaolu.
Kungiyar ta bayyana cewa za a gudanar da zanga-zangar a dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda aka gudanar da faretin ranar samun ‘yancin kai.
A jihar Legas kuwa, masu shiryawar sun ce za a yi zanga-zangar a babbar gadar Ikeja suna masu cewa dawo da tallafin mai, kudin lantarki ne kawai zai dakatar da su.
Zanga-zanga ba alheri ba ce
A zantawarmu da wasu matasa daga nan Arewa, sun bayyana cewa zanga zangar Oktoba ba za ta iya haifar da da mai ido ba, la'akari da abin da ya faru a zanga zangar baya.
Asma'u Sani Dan Kanjiba ta bayyana cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a zanga zangar Agusta, kuma an lalata dukiyar gwamnati da ta jama'a mai tarin yawa.
Asma'u Dan Kanjiba ta ce tana tsoron wasu su sake kwace zanga zangar kamar yadda aka yi a baya, inda ta ce tattaunawa da gwamnati ne mafita.
Ahmad Yahaya Dogon Baba ya ce zanga-zanga musamman wadda ke komawa tashin hankali ba ta samar da ribar abin da ake nema, sai ma dai ta kara sa abubuwa su tsananta.
Ya ce bayan gama zanga zangar Agusta, farashin kayayyaki ya tashi kuma ba shi ya hana a kara kudin man fetur ba, inda ya nemi masu shirya zanga zangar da su sake tunani.
Zanga zanga ta girgiza gwamnati
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta fara lallaba masu shirya zanga-zangar ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 domin gudun shiga wata sabuwar matsala .
Fadar shugaban ƙasa ta ce gwamnati ta fara tattaunawa da wadanda suka shirya zanga-zangar da nufin samun fahimtar juna da su kafin ranar 1 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng