Hassan Nasrallah: Dalilin da Ya Sa Kasar Isra'ila Ta Kashe Shugaban Sojojin Hezbollah
- Shugaban kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana dalilin da ya sa ya ba sojojin kasarsa umarnin kashe shugaban sojojin Hezbollah
- Netanyahu ya yi ikirarin cewa jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah ya dauko haramar sake gina karfin da Isa'ila ta kwace daga Hezbollah
- Shugaban ya ce kisan da aka yiwa Nasrallah, wani mataki ne mai muhimmaci ga Isra'ila domin samun nasara a yakin da take yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Isra'ila - Benjamin Netanyahu, firaministan Isra'ila, ya bayyana kisan da aka yi wa Hassan Nasrallah, sakatare-janar kuma shugaban kungiyar Hezbollah, a matsayin ramuwar gayya.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne sojojin Isra'ila suka sanar da cewa sun kashe Nasrallah a wani hari da suka kai ta sama.
Isra'ilaIsra'ila ta kashe jagoran Hezbollah
Hizbullah ta ce shugabanta "ya shiga cikin 'yan uwansa shahidai", inda ta kara da cewa "za mu ci gaba da yaki da makiya da kuma goyon bayan Falasdinu," inji The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda harin na ranar Juma'a ya rutsa da su akwai Abbas Nilforoushan, mataimakin kwamandan ayyuka na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran.
Wannan harin tare da mutuwar jagoran Hizbullah ba karamin tasiri zai yi ga yakin da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba, amma kungiyar ta ce ba ja baya.
Isra'ila ta fadi dalilin kashe Nasrallah
Da ya ke jawabi ga manema labarai kan ci gaban, Netanyahu ya ce Nasrallah "ba wai dan ta'adda ba ne kawai, shi kansa ta'addanci ne".
Netanyahu ya ce kisan da aka yi wa Nasrallah, wanda ya bayyana a matsayin mai kitsa yadda za a ci galabar Isra'ila, wani mataki ne mai muhimmaci ga Isra'ila domin samun nasara a yaki.
Jaridar NPR ta rahoto cewa Netanyahu ya zargi Nasrallah da laifin kashe ‘yan Isra’ila marasa adadi, da daruruwan ‘yan kasar Amurka da kuma ‘yan kasar Faransa.
"Matukar Nasrallah yana raye, to zai yi gaggawar sake gina karfin da muka kwace daga Hezbollah, shi ya sa na ba da umarnin a kashe shi."
- Inji shugaban Isra'ila.
Asali: Legit.ng