NAGGMDP: Likitoci Za Su Tsunduma Yajin Aiki a Jihar Kano, Bayanai Sun Fito

NAGGMDP: Likitoci Za Su Tsunduma Yajin Aiki a Jihar Kano, Bayanai Sun Fito

  • Kungiyar likitocin hakori ta kasa (NAGGMDP) ta yi barazanar tsunduma yajin aiki a jihar Kano daga ranar 1 ga watan Oktobar 2024
  • Kungiyar ta ce za ta shiga yajin aikin ne saboda gazawar gwamnati na cika mata alkawura yayin da ta ce likita 1 ke duba marasa lafiya 33,000
  • A zantawarmu da Dakta Shamsu Abubakar ya ce karancin likitoci da ake samu na barazana ga kiwon lafiya inda ya ba gwamnati shawara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Kungiyar likitocin hakori ta kasa (NAGGMDP) ta koka kan cewa likitoci a Kano sun yi karanci a halin yanzu tare da yin barazanar shiga yajin aikin daga 1 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin shiyya: An samu baraka tsakanin sanatoci kan bitar kundin tsarin mulki

Sakataren kungiyar NAGGMDP na jihar Kano Dr. Anas Idris Hassan ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar.

Likitoci karkashin kungiyar NAGGMDP sun yi magana kan shiga yajin aiki a Kano
Kano: Karancin likitoci da rashin cika alkawarin gwamnati zai jawo yajin aikin 'yan NAGGMP. Hoto: PeopleImages
Asali: Getty Images

Likitoci za su shiga yajin aiki

Ya bayyana cewa duk da cimma yarjejeniya da gwamnatin Kano a watannin Yuni, har yanzu ba a biya musu bukatunsu ba, lamarin da zai sa shiga yajin aikin, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hassan ya ce gwamnatin jihar ba ta magance batun alawus-alawus musamman na COVID-19 ba, wanda gwamnatin tarayya ta biya tun 2021 amma har yanzu likitocin Kano ba su karba ba.

Ya kara da cewa har yanzu sababbin likitocin da aka dauka aiki, wadanda gwamnatin jihar Kano ta dauka a watan Satumban 2023, ba su fara ganin albashinsu ba.

Babu likitoci masu yawa a Kano

Likitan ya kuma nuna damuwarsa kan yadda asibitocin Kano suka lalace da kuma rashin kayan aiki, inda ya jaddada bukatar gaggauta magance wadannan matsaloli.

Kara karanta wannan

Cin hancin N15m: Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban EFCC da wasu mutum 2

Ya yi nuni da mahimmancin daidaita adadin likitoci da marasa lafiya a Kano, wanda ya yi kasa sosai da ma'aunin Hukumar Lafiya ta Duniya.

Ya ce akwai kimanin mutane miliyan 20 a Kano, inda likitoci 600 ne kawai ke yi musu hidima, wanda hakan ya sa likita daya ne ke duba marasa lafiya 33,000.

Matsalolin rashin yawan likitoci

A zantawar Legit Hausa da Dakta Shamsu Abubakar, ya ce karancin likitoci a kowace jiha na kawo cikas ga kiwon lafiya da kuma barazana ga su kansu marasa lafiyar.

Dakta Shamsu ya ce idan ya zamana cewa likita daya ne zai duba marasa lafiya sama da 100 a rana, to ba zai samu damar yi masu binciken kwakwaf ba saboda sun yi yawa.

"Likita na bukatar ya tambayi marasa lafiya duk wani abu da ke damunsu, da bayanin iyalansa, wurin aikinsu da sauransu, amma saboda akwai tarin marasa lafiya, dole ya takaita."

Kara karanta wannan

Bayan zarginta da jefa jama'a a wahala, gwamnati ta fadi alfanun cire tallafin fetur

Likitan ya kuma ce rashin kayan aiki, rashin muhallin aiki mai kyau da kuma rashin albashi mai kyau ne suka jawo likitoci da dama ke fita kasashen waje neman aiki.

Ya ba gwamnati shawara da ta inganta walwalar likitoci ta hanyar karin albashi da alawus da kuma inganta asibitoci ta hanyar zuba kayan aiki da samar da gidajen ma'aikata.

Abba ya gana da likitocin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gana da ƙungiyar likitoci ta ƙasa (NMA) reshen jihar bayan sun tsunduma yajin aiki.

Gwamnan ya umarci likitocin da su ka dakatar da aiki a asibitin yara na Hasiya Bayero da su koma bakin aikin ceton rai da su ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.