SERAP Ta Yi Barazanar Maka INEC a Kotu, Ta Ba Hukumar Wa'adin Bincikar Gwamnoni

SERAP Ta Yi Barazanar Maka INEC a Kotu, Ta Ba Hukumar Wa'adin Bincikar Gwamnoni

  • Kungiyar SERAP ta yi barazanar maka hukumar zabe ta kasa INEC a kotu kan gaza bincikar laifuffukan zabe da zarge-zargen rashawa
  • SERAP ta ce zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar ya nuna INEC ba ta dauki darasi kan laifuffukan zaben da aka tafka a 2023 ba
  • INEC ta ba SERAP wa'adin kwanaki 7 ta kaddamar da bincike kan gwamnoni da mataimakansu kamar yadda kotu ta umarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar SERAP ta bukaci hukumar INEC da ta bi umarnin kotu na fara bincike kan zarge-zargen rashawa da magudin zabe da aka tafka a 2023.

SERAP ta bukaci shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ya tabbatar ya binciki gwamnoni da mataimakansu kan rashawa da laifuffukan zabe.

Kara karanta wannan

Cin hancin N15m: Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban EFCC da wasu mutum 2

SERAP ta yi magana kan laifuffukan zaben da aka tafka a 2023
SERAP ta ba hukumar INEC wa'adin kwanaki 7 ta binciki laifuffukan zaben 2023. Hoto: @SERAPNigeria, @inecnigeria
Asali: Twitter

Kamar yadda SERAP ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce Mai shari'a Obiora Atuegwu Egwuatu ne ya yanke hukunci a ranar 18 ga Yulin 2024 bayan ta shigar da kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SERAP ta magantu kan laifuffukan zabe

A cikin wata wasika mai kwanan wata 28 ga Satumbar 2024, dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce bai kamata INEC ta raina kotu ba.

SERAP ta ce:

“Al’amurra na cin hanci da rashawa da tashe-tashen hankula da ake tafkawa a zabuka suna yin izgili ga tsarin zaben Najeriya da kuma dimokuradiyya.
"Zarge-zarge na baya-bayan nan na laifuffukan zabe da aka yi a jihar Edo ya nuna cewa INEC ta ba ta koyi darasi daga matsalolin da aka samu a lokacin babban zaben 2023 ba."

SERAP za ta maka INEC a kotu

Kara karanta wannan

Zargin N27bn: Bayanai sun fito da hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamna

SERAP ta bukaci hukumar INEC da ta binciki zarge-zargen rashawa da laifuffukan zaben da aka tafka a 2023 kamar yadda kotun ta umarta, ko kuma ta dauki mataki.

"Za mu yi godiya idan hukumar INEC ta dauki matakan da aka ba ta shawara a kansu a cikin kwanaki 7 da karɓa ko wallafa wannan wasiƙar.
"Idan har zuwa lokacin ba mu ji ta bakinku ba, SERAP za ta shigar da kara kan raina shari'a a kan ka da INEC saboda rashin bin hukuncin kotu.”

- A cewar SERAP.

SERAP dai ta damu da cewa ci gaba da gazawar da INEC ta yi na yin biyayya ga hukuncin kotu na haifar da laifukan zabe a jihohi da dama, kamar yadda ta faru a zaben gwamnan Edo.

SERAP ta ba Tinubu wa'adi

A wani labarin mun ruwaito cewa, Kungiyar kare hakkin jama'a da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya janye karin kudin fetur.

Hukumar ta kuma ba Tinubu wa'adi na kaddamar da binciken rashawa kan kamfanin man Najeriya (NNPC) wanda ta ce shi ke kawo koma baya ga harkar man kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.