Matasa Sun Shiga Matsala Ana Shirin Zanga Zanga, Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana

Matasa Sun Shiga Matsala Ana Shirin Zanga Zanga, Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana

  • An gurfanar da matasa 10 daga aka cafke a jihohin Arewa da dama kan zargin hannu a gudanar da zanga-zanga
  • Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da matasan ne a jiya Juma'a 26 ga watan Satumbar 2024 kan tuhume-tuhume guda takwas
  • Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zanga-zanga a ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024 da ta gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sake gurfanar da matasa 10 kan zargin alaka da zanga-zanga.

Ana zargin matasan guda 10 da hannu a zanga-zangar da aka yi a ranar 1 zuwa 10 watan Agustan 2024.

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da matasa kan zargin hannu a zanga-zanga
An yasa keyar matasa 10 kan zargin hannu a zanga-zangar watan Agusta. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/@Realiyima.
Asali: UGC

Zanga-zanga: An gurfanar da matasa a kotu

Kara karanta wannan

'Babu ja da baya', Dan takarar shugaban kasa ya sha alwashin fita zanga zanga

Vanguard ta ruwaito cewa an gurfanar da su a babbar kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume guda takwas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cafke wadanda ake zargin ne daga jihohin da Kaduna da Kano da Katsina da Sokoto da Gombe da kuma Abuja.

Ana zargin matasan da ta da hankula da kuma barnar dukiyoyi yayin zanga-zangar da aka yi a watan Agusta, cewar rahoton Punch.

Zanga-zanga: Alkalin kotu ya ba da umarni

Daga bisani, alkalin kotun, Mai Shari'a, Emeka Nwite bayan sauraran korafe-korafen ya ba da umarnin sake sabunta zargin da ake yi.

Nwite ya bukaci lauyoyin wadanda ake zargin da su kawo korafi kan tuhume-tuhumen idan har akwai a kan lokaci.

Alkalin Kotun ya dage sauraran korafi kan belin zuwa ranar 4 ga watan Satumbar 2024 yayin da ya tura ranar yanke hukunci zuwa 11 ga watan Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan

Shirin zanga zanga a watan Oktoba ya girgiza gwamnatin Tinubu, an fara lallaɓa matasa

Halin kunci: Sowore ya shirya fita zanga-zanga

Kun ji cewa ana shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Omoyele Sowore ya sha alwashin jagorantar al'umma hawa tituna

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce dole su fita zanga-zangar saboda halin kunci da shugabannin suka jefa al'umma a ciki

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin sake fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024 saboda halin kunci

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.