Tinubu Ya raba N3.5bn ga Malamai, Likitoci da Sauransu, Bayanai Sun Fito
- Hukumar bada lamuni ta Najeriya CREDICORP na ci gaba da raba kudade ga ‘yan Najeriya kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi alkawari
- CREDICORP wata hukumar gwamnatin tarayya ce da aka samar domin faɗaɗa hanyoyin samun lamuni ga miliyoyin ƴan ƙasa
- Mutanen da kamfanonin da suka cancanta sun ci gajiyar shirin, kamar yadda bayanai daga hukumar gudanarwar hukumar suka nuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar ba da lamuni ta Najeriya, CREDICORP, ta raba sama da Naira biliyan 3.5 ga wadanda suka cancanci samun tallafin bashi a karkashinta.
Fredrick Nwabufo, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan hulda da jama’a ne ya bayyana haka.
CREDICORP ta raba tallafin N3.5bn
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, Nwabufo ya ce malamai, likitoci, jami’an tsaro, masu gudanarwa, da ma’aikata a ayyuka na musamman ne suka fara cin gajiyar shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nwabufo ya ce a ranar Juma’a, 27 ga Satumba, bayanai na CREDICORP sun nuna cewa an raba sama da Naira biliyan 1.5 ga ma’aikatan tarayya da na jihohi a fannin ilimi.
Mai taimaka wa shugaban kasan ya bada tabbacin cewa shirin ba da lamunin zai kara fadada domin ganin da yawan ‘yan Najeriya sun amfana a nan gaba.
Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka
Sanarwar Nwabufo ta bayyana cewa:
"Gabatar da tsarin ba da lamuni ga 'yan Najeriya ya na daya daga cikin manyan alkawurran da Shugaba Bola Tinubu ya yi a lokacin yakin neman zabensa na 2023.
"A watan Afrilun 2024, Tinubu ya amince da kaddamar da tsarin ba da lamuni na mabukata tare da kafa hukumar CREDICORP a matsayin mai kula da shirin.
"A cikin fahimtar damuwar 'yan kasa, gwamnatin Shugaba Tinubu ta ci gaba da yin duk mai yiyuwa domin bullo da tsare-tsaren ba da agaji ga 'yan Najeriya."
An dakatar da ba dalibai lamuni
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ɗage ƙaddamar da shirin bayar da lamuni ga ɗaliban Najeriya har sai baba ta gani.
Akintunde Sawyer, babban sakatare na asusun bada lamuni na Ilimi a Najeriya (NELFUND), ya sanar da dage ba da lamunin inda ya ce za a gudanar da gyare-gyare.
Asali: Legit.ng