'Yan Kasuwa Za Su Sauke Farashin Fetur yayin da Gwamnati Ta Yi Magana kan Dangote
- Manyan ‘yan kasuwa sun bayar da rahoton raguwar kudin sauke mai a kasar nan, wanda hakan na iya haifar da faduwar farashin fetur
- A cewar ‘yan kasuwar, kudin sauke mai ya ragu daga N1,300 zuwa N981 kan kowace lita, wanda a ke gani zai shafi farashin fetur
- ‘Yan kasuwar sun kuma tabbatar da shigo da kusan lita miliyan 141 na man fetur daga kasashen waje ta tasoshin ruwa guda uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Alkaluman da kungiyar manyan ‘yan kasuwar makamashi ta Najeriya (MEMAN) ta fitar sun nuna cewa kudin sauke mai ya ragu zuwa N981 kan kowace lita.
Kudin sauke mai ya kai kusan N1,130 kan kowace lita a makonnin da suka gabata, kuma ya ragu da sama da N140 a ranar 25 ga Satumba sakamakon faduwar kudin danyen mai a duniya.
Farashin danyen mai ya fadi a kasuwa
Farashin danyen mai da kuma canjin kudin kasashen waje ke taka muhimmiyar rawa wajen kayyade tsadar fetur, dizal, man jiragen sama, da kananzir, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahotanni, an yi cinikin man Brent a kan dala 80 a cikin watan Agustan 2024 amma ya sauka zuwa tsakanin $70 da $75 kan kowacce ganga a Satumba.
An sayar da man a kan dala 71.41 a ranar Alhamis, 26 ga Satumba, 2024, inda kuma ya ragu da dala 73 kan kowace ganga tun farkon wannan watan.
A cewar kididdiga, matsakaicin farashin danyen mai a watan Agusta ya kai dala 80.36 kan kowace ganga, inji wani rahoton TV360.
Biyo bayan faduwar farashin man da kuma hauhawar farashin fetur a gidajen man Najeriya, manyan ‘yan kasuwar man sun fara shigo da kayan.
'Yan kasuwa sun fara shigo da mai
Kamfanin NNPC shi ne kadai ke shigo da mai a Najeriya kafin karin farashin man fetur da kuma fara aikin matatar Dangote.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu ‘yan kasuwar man su uku suna jiran isowar kimanin lita miliyan 141 na man fetur da za a kawo Najeriya.
Dillalan dai sun bayyana cewa jiragen ruwa guda uku ne ke jigilar fetur din zuwa Najeriya biyo bayan matakin da gwamnati ta dauka kan harkar mai.
An ruwaito cewa ‘yan kasuwar sun tabbatar a ranar Alhamis 26 ga watan Satumba, 2024 cewa wasu jiragen ruwa sun iso Najeriya.
Gwamnati ta magantu kan Dangote
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matatar man Dangote za ta rika samar da lita miliyan 25 na fetur a kullum a cikin watan Satumba.
Hukumar da ke sa ido kan harkokin man Najeriya (NMDPRA) ta ce matatar Dangote za ta kara yawan litar zuwa miliyan 30 a Oktoba.
Asali: Legit.ng