‘Babu Ja da Baya’, Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Sha Alwashin Fita Zanga Zanga

‘Babu Ja da Baya’, Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Sha Alwashin Fita Zanga Zanga

  • Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Omoyele Sowore ya sha alwashin jagorantar al'umma hawa tituna
  • Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce dole su fita zanga-zangar saboda halin kunci da shugabannin suka jefa al'umma a ciki
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin sake fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024 saboda halin kunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa ya sha alwashi kan fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024.

Omoyele Sowore ya ce babu abin da zai hana shi fita zanga-zanga domin nuna damuwa kan halin da ake ciki.

Dan takarar shugaban kasa ya sha alwashin fita zanga-zanga
Omoyele Sowore ya ce babu abin da zai hana su fita zanga-zanga a ranar Talata. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Omoleye Sowore.
Asali: Twitter

Zanga-zanga: Sowore ya sha alwashin fita

Kara karanta wannan

Shirin zanga zanga a watan Oktoba ya girgiza gwamnatin Tinubu, an fara lallaɓa matasa

Sowore ya bayyana haka ne yayin hira ta musamman da jaridar Daily Trust a jiya Juma'a 27 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa zanga-zangar ta lumana ce ba tare da tashin hankali ba.

Dan gwagwarmayar ya ce za a gudanar da zanga-zangar a duka fadin Najeriya duba da yadda ake cikin yunwa.

Sowore ya ce bai tsoron zaman gidan yari

"Babu abin da zai hana mu fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024 saboda yadda gwamnati ta jefa al'umma a mawuyacin hali."
"Za a gudanar da zanga-zangar a fadin Najeriya baki daya kuma za a yi ne cikin lumana ba tare da tashin hankali ba."
"Babu abin da na ek tsoro saboda babu irin kunci da ban gani ba, an kulle ni a mulkin Muhammadu Buhari har na tsawon shekaru biyar."

Kara karanta wannan

Gangamin zanga zangar 1 Oktoba ya kankama, an mika bukatu ga Tinubu

- Omoyele Sowore

Sowore ya ce kwata-kwata bai yanzu bai tsoron zama a gidan yari saboda babu irin azabar da ba a gana masa ba.

Gwamnati ta kadu da shirin zanga-zanga

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta fara lallaba masu shirya zanga-zangar ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 domin gudun shiga wata sabuwar matsala.

Wannan dai na zuwa ne yayin da wasu ƴan Najeriya ke shirin sake fantsama kan tituna domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel