“Ku Bar Shiga Abin da ba Ku Sani ba”: Farfesa Pantami ga Malamai kan ‘Mining’
- Farfesa Isa Ali Pantami ya yi magana kan 'mining' da kuma 'kirifto' inda ya shawarci malamai su yi taka tsan-tsan
- Farfesa Pantami ya ce bai kamata malamai suna gaggawar haramta abin da ba su da cikakken ilimi a kai ba
- Shehin malamin ya ce gagawar haramta abubuwa ke mayar da duniyar Musulunci baya a bangaren fasaha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe - Shiekh Isa Ibrahim Pantami ya shawarci malamai kan shiga lamarin da ba su da cikakken ilimi a kai.
Farfesa Pantami na magana ne kan 'mining' da 'kirifto' duba da yadda wasu malamai ke halattawa ko haramtawa.
Mining: Farfesa Pantami ya shawarci malamai
Pantami ya tabbatar da haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin karatuttukan malaman sunna ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehin malamin ya nuna damuwa kan yadda gaggawar haramta irin wannan babban lamari ke kawo ci baya ga duniyar Musulunci.
"Ba na daga cikin mutane da ke haramtar da komai da komai a cikinsa, ina tunatar da wadanda ake yi wa tambaya, don Allah mu dena gaggawar ba da fatawa kan abin da ba mu da cikakken ilimi a kansa."
"Na ji wasu sun haramta 'Bitcoins' wasu sun haramta 'Blockchain Technology' ya kamata mu bar haramta abu a bangaren da ilimi bai ishe mu ba."
"Irin gaggawar haramta abin da ilimi bai ishe mu ba ya ke mayar da duniyar Musulunci baya a bangaren fasaha."
- Malam Isa Ali Pantami
"Matsalolin da fatawar gaggawa ke jawowa" - Pantami
Malamin ya koka kan yadda malamai ke gaggawar haramta abubuwan zamani da suka shigo wanda harkoki ne na cigaba a rayuwar dan Adam.
Farfesa Pantami ya ce rashin adalci ne za ka yi fatawa sai ka dauko wanda bai gama kwarewa ba a bangaren ba.
Ya ce kamata ya yi ka dauko wanda ya kware matuka a bangaren domin yi masa tambayoyi tare da fadin matsayar addini.
Legit Hausa ta tattauna da wani masani a harkar 'mining' inda ya ce tabbas maganar Malam gaskiya ne da yawa ba su fahimci harkar ba.
Muhammed Auwal A. ya ce mafi yawan malamai ba su yin bincike kan lamarin wanda hakan ke saka shakka a fatawowin da suke bayarwa.
Ya ce idan har masana suka haramta 'mining' da 'kirifto' dole su ma za suamu mafita saboda bin umarnin addini.
Hukumomin asibiti sun haramta 'Mining' a bakin aiki
Mun baku labarin cewa yayin da harkokin 'kirifto' da 'mining' suka zama ruwan dare, hukumomi sun fara daukar matakai kan lamarin.
Asibitin Gwamnatin Tarayya (FTH) da ke Gombe ya haramtawa ma'aikata 'kirifto' da 'mining' yayin da suke bakin aiki.
Asali: Legit.ng