Jigon APC Ya Yi Nasara kan Gwamnan PDP da Kotu Ta Yi Watsi da Matakinsa
- Bayan rashin nasara a zaben gwamnan jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya sake samun matsala a kotu kan sha'anin gona
- Jigon APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu shi ya maka gwaman a kotu da zargin kwace masa gonaki ba tare da ka'ida ba a jihar
- Alkalin kotun, Peter Akhihiero ya yi fatali da matakin da gwamnan ya dauka na kwace gonakin Ize-Iyamu a karamar hukumar Oredo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Babbar kotun jihar Edo ta yi zama kan shari'ar jigon APC, Osagie Ize-Iyamu da Gwamna Godwin Obaseki.
Kotun karkashin jagoracin Mai Shari'a, Peter Akhihiero ta rusa matakin Obaseki na kwace kadarorin Ize-Iyamu.
Jigon APC ya maka gwamnan PDP a kotu
The Nation ta ruwaito cewa Ize-Iyamu ya shiga kotu ne bayan Obaseki ya kwace wasu gonakinsa a karamar hukumar Oredu da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta dakatar da gwamnatin jihar da mukarrabansa daga sake shiga hurumi ko kuma yin wani abu ga Ize-Iyamu da zai shiga masa hakkinsa.
Har ila yau, kotun ta ci tarar gwamnatin jihar N5m saboda gwamnan da kwamishinan shari'a da hukumar EdoGIS suna wuce gona da iri a lamarin Ize-Iyamu tun watan Yulin 2021.
Yaushe Obaseki ya kwace gonar Ize-Iyamu?
Tun a watan Yulin 2021 ne Gwamna Obaseki ya kwace gonakin Ize-Iyamu wanda jigon APC ya kalubalanci matakin, cewar rahoton Tribune.
Ize-Iyamu dai a baya ya rike mukamin Sakataren Gwamnatin jihar kuma ya nemi takarar gwamnan jihar karkashin PDP a shekarar 2016 da 2020.
Har ila yau. Ize-Iyamu ya janye daga neman takarar gwamnan a watan Faburairun 2024 awanni kafin zaben fidda gwani.
Shaibu ya caccaki Gwamna Obaseki na Edo
Kun ji cewa jigon APC kuma mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya sake caccakar Gwamna Godwin Obaseki.
Shaibu ya ce ko kadan bai rike Obaseki a zuciyarsa ba duk da abubuwan da suka faru a baya inda ya ba shi shawara.
Ya ce gwamnan bai taba cin zabe ba sai da taimakonsu inda ya ce rasa karamar hukumarsa ya tabbatar da haka.
Asali: Legit.ng